Idan Na Tona Asirin Ayu, Ko 'Yayansa Sai Sun Guje Masa: Wike

Idan Na Tona Asirin Ayu, Ko 'Yayansa Sai Sun Guje Masa: Wike

  • Gwamnan Wike ya sake dira kan shugaban jam'iyyar adawa ta PDP, Sanata Iyorchia Ayu
  • Gwamnan na Rivers ya sake fallasa sabuwar zargin rashawa cewa Ayu ya karbi N100m hannun wani gwamna
  • Wike ya lashi takobin cewa ba zasu daina kira ga tsige Ayu ba ko da ko hakan zai kai ga faduwar PDP

Port Harcourt - Gwamnan jihar Rivers Nyesom Wike ya sake tsokano shugaban uwar jam'iyyar PDP, Iyorchia Ayu, kan zargin almundahanar da yayi masa a watan Satumba.

Wike ya kara yanzu da cewa Ayu fa ya karbi milyan dari hannun wani gwamna, sannan ya koma wajen kwamitin gudanarwa ya sake karban wani milyan dari.

Wike ya bayyana hakan yayin hira da yan jaridar ranar Juma'a a birnin Port Harcourt.

Kara karanta wannan

Bayan Goyon Bayan Gwamna APC, Sabbin Bayanai Sun Fito Kan Yuwuwar Wike Ya Fice PDP

Karo na biyu, Gwamnan jihar Rivers ya hau minbarin fara tonon silili kan wasu jiga-jigan jam'iyyar Peoples's Democratic Party PDP.

Wikey AYu
Idan Na Tona Asirin Ayu, Ko 'Yayansa Sai Sun Guje Masa: Wike
Asali: Facebook

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

A cewarsa:

"Ayu ya karbi N100m hannun wani gwamna don aiki cibiyar demokradiyyar PDP, sannan ya koma wajen NWC ya sake karban N100m duk na aiki daya."
"Idan ya karyata zan fada muku sunan Gwamnan da ya bashi kudin."
"Baicin soyayyar da mukewa jam'iyyar nan, idan muka fadi wasu abubuwa, har 'yayan Ayu sai sun guje masa."

Yau Zan Kara Adadin Hadimaina Zuwa 100,000: Gwamna Nyesom Wike

A wani labarin kuwa, Gwamnan jihar Ribas, Nyesom Wike ya bayyana cewa zai kara adadin nade-naden hadimansa a fannin siyasa daga 50,000 zuwa 100,000.

Wike ya bayyana hakan ne ranar Juma'a, 14 ga Oktoba yayin zaman da yayi da yan jarida a gidan gwamnatin jihar.

Kara karanta wannan

Duk Jam'iyyar Dake Takara Da APC a Legas 'Batawa Kanta Lokaci Take, Wike

Wannan ya biyo bayan cece-kuce da akeyi cewa gwamnan na baiwa mutane mukamai yayinda yake da sauran yan watanni ya sauka daga mulki.

Asali: Legit.ng

Authors:
AbdulRahman Rashida avatar

AbdulRahman Rashida

Tags: