Kai Tsaye: Karo na 2, Wike Ya Fara Zaman Tonon Silili Kan Jam'iyyar PDP
Karo na biyu, Gwamnan jihar Rivers ya hau minbarin fara tonon silili kan wasu jiga-jigan jam'iyyar Peoples's Democratic Party PDP a yau Juma'a.
Gwamnan jihar Rivers, Nyesom Wike, ya gayyaci yan jaridun manyan gidajen jarida hudu don yi masa tambayoyi kan abubuwa dake gudana a jam'iyyar Peoples Democratic Party (PDP).
Ana zaman ne a fadar gwamnatin jihar dake Fatakwal yanzu haka.
Atiku shima dan neman rigima ne, tun 2014 na samu lambar girmamawan CON
Gwamna Nyesom Wike Yayi martani kan jawabin dan takaran shugaban kasan PDP, Atiku Abubakar, idan yace ya tabbata cewa bai yi zaben tumun-dare ba wajen dauka Okowa.
Atiku ya bayyana hakan ne yayin taya Ifeanyi Okowa murnar samun ambar girmamawan CON.
Wike yace ya samun labarin abinda Atiku ya fada kuma wannan tsokana ne. Yace shi fa tun shekarar 2014 ya samu wannan lambar girma da ake ta fankamawa yanzu.
Ina wa dukkan yan takaran PDP aiki, ciki har da Atiku
Nyesom Wike ya jaddada cewa ba zasu amince da cigaba da zaman Iyorchia Ayu ba amma duk da haka yana yiwa dukkan yan takaran PDP aiki na yakin zaben 2023.
Ayu fa babban barawo ne dan damfara, Ya karbi N100m hannun wani gwamna
Gwamna Wike ya sake tsokano shugaban uwar jam'iyyar PDP, Iyorchia Ayu, kan zargin almundahanar da yayi masa a watan Satumba.
Wike ya kara yanzu da cewa Ayu fa ya karbi milyan dari hannun wani gwamna, sannan ya koma wajen kwamitin gudanarwa ya sake karban wani milyan dari.
A cewarsa:
"Ayu ya karbi N100m hannun wani gwamna don aiki cibiyar demokradiyyar PDP, sannan ya koma wajen NWC ya sake karban N100m duk na aiki daya."
"Idan ya karyata zan fada muku sunan Gwamnan da ya bashi kudin."