Kotu Ta Wanke Nnamdi Kanu Amma Bata Ce Mu Sakeshi ba, AGF Malami
- Ministan Shari'a, Malami, ya yi martani kan hukuncin kotun da ta wanke Nnamdi Kanu jiya
- Abubakar Malami yace kotu bata ce a saki Nnamdi Kanu ba, akwai sauran laifuka a kansa na kafin ya gudu
- Gwamnatin Najeriya ta sankamo Nnamdi Kanu daga kasar Kenya kuma tun lokacin ta garkameshi wajen DSS
Abuja - Antoni-Janar na tarayya kuma Ministan Shari'a, Abubakar Malami, a ranar Alhamis ya yi tsokaci kan hukuncin kotun daukaka kara da ta wanke Nnamdi Kanu.
Nnamdi Kanu shine jagoran kungiyar rajin kafa kasar Biyafara watau IPOB.
A jawabin da mai magana da yawunsa, Dr. Umar Jibril Gwandu, ya fitar, Mr Malami ya ce kawai kotu ta wanke Kanu ne amma bata ce a sakeshi, rahoton ChannelsTV.
Yace:
DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar
"Ofishin Antoni Janar na tarayya kuma Ministan Shari'a ta samu labarin kotun daukaka kara game da Nnamdi Kanu."
"Amma fa a sani, kawai an wanke Kanu ne amma ba'a sake shi ba."
"Saboda haka, zamu dauka matakai kuma zamu yiwa jama'a bayanai lokacin da ya kamata."
"Abinda kotu ta yanke hukunci kai shine yadda aka dawo da shi Najeriya, amma a fahimci cewa akwai wasu lamuran da ake zarginsa da su kafin guduwan da yayi."
Kotun Daukaka Kara Ta Wanke Nnamdi Kanu, Ta Yi Watsi da Karar Gwamnati
A ranar Alhamis, Kotun daukaka kara dake zamanta a Abuja ta yi watsi da zargin ta'addanci da gwamnatin tarayya keyi kan shugaban kungiyar rajin kafa kasar Biafra, Nnamdi Kanu.
Alkalan kotun a ranar Alhamis su uku su kara da cewa dauko Nnamdi Kanu da gwamnati tayi daga kasar Kenya ya sabawa doka.
Lauyan Kanu, Ifeanyi Ejiofor, a jawabin da ya fitar a shafinsa na Tuwita
Asali: Legit.ng