An Damke Wani Matashi Da Wandon Hailan Mata Guda Uku A Jihar Ogun

An Damke Wani Matashi Da Wandon Hailan Mata Guda Uku A Jihar Ogun

  • Wani matashi da ake zargin dan kungiyar asiri ne ya shiga hannun jami'an tsaron Amotekun
  • Har yanzu ana fama da matsalar yin amfani da kayan al'adan yan mata wajen tsafe-tsafe
  • Jami'an hukumar sun mikashi ga jami'an yan sanda don zurfafa bincike da kuma hukuntashi

Abeokuta - Jami'an tsaron Amotekun dake jihar Ogun sun damke wani matashi mai suna Felix Ikpeha da wando 'yar ciki na mata guda uku jike da jini.

An damke Ikpeha, wanda dan asalin Warri a jihar Delta ne a unguwar Imo-Ayo dake Ajibawo Afan Ota, kramar hukumar Ado-Odo/Ota ta jihar.

Kwamandan Amotekun na jihar, David Akinremi, ya bayyana hakan ranar Alhamis a jawabin da ya fitar a Abeokuta, babbar birnin jihar.

Kara karanta wannan

An Kama Korarrun Ma'aikata Da Suka Yi Yunkurin Sace Tsohon Mai Gidansu Saboda Ya Sallame Su Daga Aiki

Jihar Ogun
An Damke Wani Matashi Da Wandon Hailan Mata Guda Uku A Jihar Ogun
Asali: Getty Images

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Akinremi yace an damke matashin ne yayin al'ummar suka zargi take-takensa.

Yace:

"Yayinda ake bincikesa, an ganshi da wandon hailan mata uku kuma ya gaza bayanin inda ya same su."
"Daga baya yace cikin Bola ya tsincesu, amma ya manta inda ya dauko."

Kwamanda Akinremi ya yi bayanin cewa ana zargin Ikpeha na cikin wata kungiyar asiri masu tsafin kudi.

Yace an turashi wajen hukumar yan sanda domin gudanar da bincike da kuma hukuntashi.

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel