Nan Da Disamba Matsalar Tsaro Za Ta Zama Tarihi, Gwamnatin Tarayya
- Gwamnatin tarayya ta yi alkawarin cewa nan da karshen shekarar nan za'a kawar matsalar tsaro gaba daya
- Ministan harkokin cikin gidan ya ce Buhari yayi umurnin a kawar da matsalar zuwa Disamba
- Shugaba Buhari da kansa ya yi alkawarin kawar da matsalar tsaro kafin ya sauka daga mulki
Abuja - Ministan harkokin cikin gida, Rauf Aregbesola, ya bada tabbacin cewa za'a magance dukkan matsalolin tsaron Najeriya nan da watan Disamban shekarar nan.
Aregbesola, ya yi kira ga yan Najeriya su taimakawa jami'an tsaro wajen kai rahoton duk wani wanda suke zargi.
Ministan ya bayyana hakan ne yayin tattaunawa da kamfanin dillancin labarai (NAN) a Abuja ranar Talata, rahoton TheNation.
Ministan yace:
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
"Buhari ya bada umurnin kawar da dukkan masu yiwa Najeriya da dukiyarsu barazana nan da Disamba."
"Kowa na iyakan kokarinsa don tabbatar da cewa an magance wadannan matsalolin."
"Muna kan aiki. Zamu kawar da dukkan matsalolin tsaro nan da Disamba."
Aregbesola yace da yan ta'addan Boko Haram dake guduwa daga Arewa maso gabas ne ke aikata garkuwa da mutane.
Buhari: Sai Na Magance Matsalar Tsaro Kafin Na Sauka Daga Mulki
Shugaba Muhammadu Buhari ya yi alƙawarin cewa a cikin sauran kwanakin da suka rage masa a matsayin shugaban ƙasa, ƴan Najeriya za su ga sauyi game da matsalar tsaro.
Shugaban ya ba da wannan tabbaci ne a ranar Juma’ar nan da yake gabatar wa da Majalisar ƙasa tsararren jadawalin kasafin kuɗin Naira tiriliyan ashirin da dubu ɗari biyar da hamsin da ɗaya.
Najeriya dai ta daɗe tana shan fama game da matsalolin tsaro da ya haɗa da na Boko Haram a Arewa maso Gabas da na tsaginta, wato ISWAP.
Asali: Legit.ng