Ku Kiyayi Wadanan Magungunan Na Tari: Hukumar Lafiya WHO Ta Jerantosu

Ku Kiyayi Wadanan Magungunan Na Tari: Hukumar Lafiya WHO Ta Jerantosu

  • Hukumar lafiya ta duniya ta lissafo wasu magungunan Syrup na tari masu haddasa ciwon koda cikin yara
  • Kimanin kananan yara 70 ne suka hallaka yanzu a kasar Gambiya sakamakon shan wannan magunguna
  • Hukumar NAFDAC ta Najeriya tace wadannan magunguna basu da rijista a fadin Najeriya

Ekiti - Shugaban kungiyar kwamishanonin lafiya a Najeriya, Dr Oyebanji Filani, ya gargadi yan Najeriya kan amfani da wasu magungunan tari dake hallaka mutane.

Ya ce wadannan magunguna sun hallaka yara sama da 66 a kasar Gambiya, Afrika ta yamma, rahoton Punch.

Oyebanji wanda shine kwamishanan lafiyan jihar Ekiti, ya bayyana hakan ne a jawabin da ya fitar ranar Talata.

Ya yi kira ga iyaye su garzaya da duk yaron da ya fara ciwon kai da gudawa bayan shan wani maganin tari.

Kara karanta wannan

Ooni Na Ife Ya Sake Angwancewa Da Kyakkyawar Budurwa Karo Na 3 Cikin Makonni

Oyebanji ya ce kungiyar lafiyar duniya ta bada umurnin cire wadannan magunguna daga kasuwanni.

Syrup
Ku Kiyayi Wadanan Magungunan Na Tari: Hukumar Lafiya WHO Ta Jerantosu
Asali: Getty Images

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

A cewarsa, magungunan sun hada da:

1. Promethazine Oral Solution BP,

2. Kofexmalin- Baby Cough syrup,

3. MAKOFF Baby and MaGrip n Cold Syrup

Yace:

"Dirakta Janar na WHO, Dr Tedross Ghebreyasus, ya ce wadannan magungunan na dauke da wasu sinadari biyu masu illa kuma yana kawo ciwon koda cikin yara."
"WHO ta kara da cewa wadannan sinadarai ba a iya ganinsu ko shakansu shiyasa suke da wahalan sha'ani."

Dr Oyebanji ya kara da cewa Shugabar hukumar kula da lafiyar abinci da magunguna NAFDAC, Prof Mojisola Adeyeye, ta tabbatar da cewa wadannan magunguna basu da rijista a Najeriya.

Yace:

"Zamu cigaba da aiki da NAFDAC da sauran hukumomi wajen tabbatar da cewa za'a kwashe wadannan magunguna duk inda aka gansu don lafiyan yan Najeriya."

Kara karanta wannan

An Kama Fursunan Da Ya Tsere Daga Kuje Ya Yada Zango A Kano

Asali: Legit.ng

Online view pixel