Ranar Alhamis Za Muyi Ganawar Gaggawa DOn Yanke Shawara Kan Yajin Aiki
- Da alamun lamarin yajin aikin ASUU na gab da zuwa karshe yayinda shugabanninta zasu zanna
- Ana kyautata zaton cewa shiga tsakanin da kakakin majalisar wakilai yayi zai haifar da 'da mai ido
- Ana sa ran shugaba Buhari ya fitar da jawabi yau Talata bisa yadda sukayi da kungiyar ASUU
Kungiyar Malaman jami'o'in Najeriya ASUU zata yi ganawar gaggawa na majalisar zartaswarta ranar Alhamis domin tattauna yadda tayi da gwamnatin tarayya.
Gabanin wannan zama da za'a yi a hedkwatara dake Jami'ar Abuja UNIABUJA, kungiyar ta umurci rassanta su gana da mambobinsu don jin ra'ayinsu.
Bayan zaman da za'ayi ranar Alhamis, da yiwuwan a janye yajin aikin da dare ko kuma safiyar ranar Juma'a.
Wannan rahoto ya biyo bayan jita-jitan da ake yadawa na cewa ASUU ta janye daga yajin aiki.
Shugaban kungiyar, Farfesa Emmeneul Osodeke, a martaninsa yace sam basu janye ba, har yanzu suna kan bakansu, rahoton Vanguard.
Yace amma suna gab da janyewa bayan sakamakon da ya fito daga zaman mambobinsu.
DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka
Yajin aikin ASUU na gab da zuwa karshe
Femi Gbajabiamila ya tabbatarwa 'yan Najeriya cewa, nan kusa kadan kungiyar malaman jami'a za ta koma bakin aiki.
Kakakin na majalisa ya bayyana hakan ne a ganawarsa da shugaban ASUU, Fafesa Emmanuel Osodeke da sauran kusoshin kungiyar da yammacin yau Litinin 10 ga watan Oktoba.
A cewarsa, Yau Shugaba Buhari zai bayyana yadda zaman sulhun ya gudana. Hakazalika, kungiyar ta ASUU ta kuma bayyana godiya da yabo ga majalisar wakilai bisa tsoma baki tare da kawo mafita ga yajin aiki.
Asali: Legit.ng