Atiku Zai Lashe Zaɓen Shugaban Kasa da Ƙuri’u Miliyan 7 a 2023, Iyorchia Ayu

Atiku Zai Lashe Zaɓen Shugaban Kasa da Ƙuri’u Miliyan 7 a 2023, Iyorchia Ayu

  • Jam’iyyun na cigaba da nuna ƙwarin guiwarsu game da ƴan takarkarunsu, musamman ma na shugabancin ƙasa
  • Shi ma shugaban jam’iyyar PDP na ƙasa, ya yi kurarin cewa jam’iyyar za ta lashe zaɓe da tazarar kuri’u har miliya bakwai a wajen wani taro da Jam’iyyar ta gudanar
  • Sai dai duk da samun halartar jiga-jigan jam’iyyar PDP na ƙasa da aka samu a wurin taron, Gwamnan River, Wike, bai halarta ba wanda ke nuni da cewa an bar baya da ƙura a siyasance

A cewar shugaban jam’iyyar PDP ta ƙasa, Iyiorcha Ayu, ya tabbatar da cewa ɗan takarar jam’iyyar, Atiku Abubakar, zai ba wa mutane mamaki, domin zai lashe zaɓen ne da zunzurutun tazara ta ƙuri’a har miliyan bakwai a tsakaninsa da sauran ƴan takara.

Kara karanta wannan

Lokaci Ya Yi: Wata Budurwa Yar Shekara 18 Dake Kan Ganiyarta Ta Mutu a Hotel

Shugaban jam’iyyar na wannan iƙirari ne a yayin wani zama na masu ruwa da tsaki da aka gudanar a ranar Laraba a babban ɗakin taro na wasanni da ke jihar Bauchi.

Ko da a ranar, sai da ɗan takarar ya yi nasarar karɓar dubun nan magoya baya da suka canja sheƙa daga wasu jam’iyyun zuwa PDP a wani taro da aka yi rana ɗaya da wajen zama na masu ruwa da tsakin.

Iyorchia
Atiku Zai Lashe Zaɓen Shugaban Kasa da Ƙuri’u Miliyan 7 a 2023, Iyorchia Ayu Hoto: PDP
Asali: Twitter

Jaridar Punch ta ruwaito cewa Atiku Abubakar ya iso wajen taron ne tare da mataimakinsa Ifeanyi Okowa da Shugaban Jam’iyyar PDP na ƙasa Iyiorcha Ayu da shugaban majalisar gwamnonin Najeriya da kuma babban daraktan kamfen na gwamnan Sakkwato, wato Aminu Waziri Tambuwal har da ma tsohon mataimkin shugaban ƙasa, Namadi Sambo.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Har’ila yau wannan tawaga ta ƙushi mutane kamar gwamnan Bauchi, Bala Muhammad da na Adamawa, Umaru Fintiri da na Taraba, Darius Ishaku da mataimakansu. Sannan akwai tsohon gwamnan jihar Jigawa, Alh. Sule Lamiɗo da Boni Haruna da Ibrahim Ɗankwambo. Ga kuma tsohon shugaban sanatocin Najeriya, Bukola Saraki da sauransu.

Kara karanta wannan

Da Duminsa: Bayan Shafe Watanni Uku, Yan Bindiga SUn Saki DPOn Yan Sandan Da Suka Sace

Shugaban Jam’iayyar, a yayin da yake magana da jagororin jam’iyyar na Arewa maso Gabas ta PDP, ya bayyana cewa baya son jin wai jam’iyyar ta yi ƙarfi ne kawai a kafafen sada zumunta ko kuma a kafafen Talabijin.

Sannan ya bayyana fargabarsa game da tunanin rashin samun halartar jama’a. “a yayin da muke tahowa, na shiga zullumin ko ba za a samu halartar mutane wannan yanki wurin taron ba,domin mutane ne jam’iyya ba, shuwagabannin ita jam’iyyar.

Sai dai fa tsuguno ba ta ƙare ba, domin kuwa ba a samu halartar gwamnan jihar Rivers ba, Nyesome Wike ko makusancinsa wanda hakan ke cigaba da nuni da irin rikicin cikin gida da jam’iyyar ke cigaba da fama da shi.

Asali: Legit.ng

Online view pixel