Tikitin Musulmi Da Musulmi: Ba Zan Taba Zaben Tinubu Ba, Cardinal Onaiyekan

Tikitin Musulmi Da Musulmi: Ba Zan Taba Zaben Tinubu Ba, Cardinal Onaiyekan

  • John Cardinal Onaiyekan ya lashi takobin cewa ba zai zabi dan takaran shugaban kasan APC ba
  • Babban Malamin Cocin Katolikan yace tun da APC ta yanke shawaran yin Musulmi da Musulmi, ba zai zabesu ba
  • Dan takaran shugaban kasa jam'iyyar APC, Tinubu da mataimakinsa, Shettima, duk Musulmai ne

Osun - .Tsohon Archbishop din Abuja, John Cardinal Onaiyekan, a ranar Laraba ya lashi takobin cewa ba zai taba zaben dan takara shugaban kasan jam'iyyar All Progressives Congress (APC), Bola Tinubu, ba.

Onaiyekan yace dalilin yanke wannan shawara shine saboda Tinubu ya zabi Kashim Shettima wanda yake Musulmi matsayin mataimakinsa.

Ya bayyana hakan ne a lakcan da yayi ranar Laraba a Cocin Katolikan St. Kizito Pastoral Centre, dake Ede jihar Osun, rahoton Tribune.

Kara karanta wannan

Gwamnan Jihar Bauchi Ya Bayyana Wanda Zai Lashe Zaben Shugaban Kasa a 2023

Cardinal
Tikitin Musulmi Da Musulmi: Ba Zan Taba Zaben Tinubu Ba, Cardinal Onaiyekan

A cewarsa, APC ta yanke shawaran amfani da tikitin Musulmi da Musulmi don manufar cin zabe saboda haka shima ba zai zabi Musulmi ba.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Yace:

"Katin zabe 'daya gareni, kuma da Ikon Allah ba zan zabi Musulmi ba. Shawarar da na yanke kenan."
"Akwai mambobin cocinmu a APC, har da manya cikinsu. APC ta nada Gwamnan jihar Plateau Simon Lalong matsayin Diraktan kamfe kuma dan Katolika ne, wannan zabinsa ne."
"A tsarin cocinmu, bamu shiga harkar siyasa."

Asali: Legit.ng

Authors:
AbdulRahman Rashida avatar

AbdulRahman Rashida

Tags: