Cikakken Jerin Sunayen Sabbin INEC REC Da Majalisa Ta Amince Da Su Jiya

Cikakken Jerin Sunayen Sabbin INEC REC Da Majalisa Ta Amince Da Su Jiya

A ranar Laraba, 6 ga Oktoba, Majalisar Dattawa ta amince da dukkan mutum 19 da Shugaba Muhammadu Buhari ya zaba matsayin kwamishanonin jiha na hukumar zabe INEC gabanin zaben 2023.

Majalisar ta yi watsi da takardun zarge-zargen da aka yiwa wasu daga cikin wadanda Buhari ya nada saboda yan jam'iyyar All Progressives Congress (APC) ne.

Majalisar tace babu kwararan hujjoji dake nuna cewa gaskiyar zargin da ake musu.

Ahmad
Cikakken Jerin Sunayen Sabbin INEC REC Da Majalisa Ta Amince Da Su Jiya Hoto: Nigerian Senate
Asali: Facebook

Daga cikin mutum 19 da Buhari ya mika sunayensu, 5 sake nadasu akayi yayinda 14 sabbi ne, a cewar Premium Times.

Ga jerinsu:

  1. Ibrahim Abdullahi (Adamawa)
  2. Obo Effanga (Cross River)
  3. Umar Ibrahim (Taraba)
  4. Agboke Olaleke (Ogun)
  5. Samuel Egwu (Kogi)
  6. Onyeka Ugochi (Imo)
  7. Muhammad Bashir (Sokoto)
  8. Ayobami Salami (Oyo)
  9. Zango Abdu (Katsina)
  10. Queen Elizabeth Agwu (Ebonyi)
  11. Agundu Tersoo (Benue).
  12. Yomere Oritsemlebi (Delta)
  13. Yahaya Ibrahim (Kaduna)
  14. Nura Ali (Kano)
  15. Agu Uchenna (Enugu)
  16. Ahmed Garki (FCT)
  17. Hudu Yunusa (Bauchi)
  18. Uzochukwu Chijioke (Anambra)
  19. Mohammed Nura (Yobe).

Kara karanta wannan

Fushin Gwamnoni: Shugaban APC Na Ƙasa Ya Faɗi Babban Abinda Zai Sa Tinubu Ya Sha Kaye a Zaɓen 2023

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

An zargi wasu cikin yan jam'iyyar APC ne

Legit.ng ta tattaro cewa wasu kungiyoyin sa kai sun tuhumci wasu daga cikin wadannan mutum 19 da alaka da wasu jam'iyyun siyasa.

Sun ce Muhammad Bashir, dan jihar Sokoto ya yi takarar gwamnan karkashin APC a 2015.

Hakazalika Sylvia Agu, yar jihar Enugu ana zargin kanwar mataimakin shugaban jam'iyyar APC ne na yankin kudu maso gabas.

Kungiyar tace Pauline Onyeka, a baya an tuhumceta da rashawa tare da hadin kai da yan siyasa wajen magudin zabe.

Dalilin da yasa aka amince da su duk da zarge-zargen

Shugaban kwamtin majalisa kan INEC, Kabiry Gaya, ya tabbatar da cewa lallai an zargi wasu mutane cikin wadanda Buhari ya aike sunayensu, rahoton ThisDay.

Amma yace lokacin tantancesu, ba'a samu wani kwakkwarin hujjan dake nuna cewa suna da alaka da jam'iyyun siyasa.

Kara karanta wannan

Yanzu Haka: Shugaban APC Ya Shiga Ganawar Sirri Da Gwamnonin APC 6 Kan Rikicin Kwamitin Kamfe

Gaya yace:

"Babu wani kwakkwarin hujja ko takardar rantsuwa daga garesu dake nuna cewa mambobin wata jam'iyya ne."

Asali: Legit.ng

Authors:
AbdulRahman Rashida avatar

AbdulRahman Rashida

Tags: