Kotu Ta Yi Wa Ƙwararren Ɗan Ƙwallon Najeriya Ɗaurin Shekaru 12 Kan Laifan Damfara Ta Intanet

Kotu Ta Yi Wa Ƙwararren Ɗan Ƙwallon Najeriya Ɗaurin Shekaru 12 Kan Laifan Damfara Ta Intanet

  • Kotu da zamanta a Ilorin ta yanke wa wani ɗan kwallon Najeriya, Jacob Wisdom Chukuemeka hukuncin daurin shekara 12 a gidan yari
  • Hakan na zuwa ne bayan da hukumar EFCC ta gurfanar da shi a kotu kan mallakar kudade ta hanyar damfara
  • Kotun ta kwace wasu daga cikin kadarorin dan kwallon ta ce a saka a Baitil Mali sannan ta bashi zabin biyan tara na kudi

Ilorin - An yanke wa ƙwararren ɗan kwallo, Jacob Wisdom Chukuemeka hukuncin daurin shekaru 12 kan laifuka masu alaka da damfara ta intanet da mallakar kudaden haram.

Mai shari'a Mohammed Sani na Babban Kotun Tarayya da ke zamanta a Ilorin, jihar Kwara a ranar Litinin, 4 ga watan Oktoban 2022, a cewar hukumar ta EFCC.

Kara karanta wannan

Rudani: Bayan dogon nazari, kotu ta wanke Magu daga zargin almundahana

Dan Kwallo
Kotu Ta Yi Wa Ƙwararren Ɗan Ƙwallon Najeriya Ɗaurin Shekaru 12 Kan Laifan Damfara Ta Intanet. Hoto: @officialEFCC.
Asali: Twitter

An daure Chukuemeka ne bayan ya amsa laifin tuhumar biyu na mallakar kudin haram da ake masa bayan da hukumar EFCC ta gurfanar da shi.

Daya daga cikin tuhumar ta ce:

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

"Kai, Jacob Wisdom Chukuemeka daga ranar 6 ga watan Mayun 2021 zuwa 22 ga watan Afrilun 2022 ka mallaki N792,454.00 (Dubu dari bakwai da casa'in da biyu, ɗari huɗu da hamsin da hudu) a asusun bankin ka ɗaya daga cikin bankunan zamani a Najeriya kuma ka san na haram ne don haka ka aikata laifi da ya saba wa sashi na 17 (a) da (b) na dokar EFCC, Act 2004."

Wanda ya ake zargin ya amsa laifin sa bayan da aka karanto masa.

Bayan amsa laifin da ake tuhumarsa, Aliyu Adebayo, lauya mai gabatar da kara ya bukaci kotu ta yanke masa laifin da aka gurfanar da shi a kai.

Kara karanta wannan

Da dumi-dumi: Hukumar 'yan sanda ta kori wasu manyan jami'anta 7, ta ragewa 10 girma

Hukuncin kotu

A hukuncin da ya yanke, Mai shari'a Sani yanke masa hukuncin daurin shekaru uku a laifin farko da na biyu. Amma ya bashi zabin biyan tara ta N794,545.00 a laifin farko da N300,000 a laifi na biyu.

An kuma kwace wayarsa Iphone 11 da ya yi amfani da shi wurin aikata laifin da kuma N250,000.

Har wa yau, kotun ta umurci wanda aka yanke wa hukuncin ya mayarwa wanda ya damfara N524,545.00 saurin kudin da ya damfare shii.

Asarinsa ya tonu ne lokacin da jami'an EFCC suka kama shi a Ilorin saboda mallakar kudi da ake zargin na haram ne a asunsunsa kuma ya kasa bayanin inda ya samo kudin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164