Cosmas Maduka: Attajirin Da Bai Taɓa Zuwa Makaranta Ba, Ko Talabijin Bai Da Shi

Cosmas Maduka: Attajirin Da Bai Taɓa Zuwa Makaranta Ba, Ko Talabijin Bai Da Shi

  • Wani attajiri Cosmas Maduka, shugaban kanfanin Coscharis Group ya ba da labari game da rayuwarsa
  • Ya bayyana hakan ne a yayin wani taro, inda ya ba wa mutane mamaki bayan bayyana cewa shi ko Talabijin bai kallo
  • Sannan attajirin ya ba wa matasa shawara da suke fatan yin nasara da kuma zama attajirai

Shahararen attajirin nan Cosmos Maduka, mamallakin kanfanin Coscharis Group, ya ba wa mutane mamaki a yayin wani taro a cocin Calvary Bible Church da ke Idimu na jihar Lagos da ya bayyana cewa ko akwatin talabijin bai da shi.

Ya ce rashin mallakar Talabijin ɗin abu ne na ra’ayin ƙashin kai, amma hakan na nuna irin yadda ya yi nasara a rayuwa ke mai da hankali kan wasu al’amura da suka fi muhimmanci. Sannan ya shawarci mutane da su kasance masu manufa da kuma tsara rayuwarsu.

Kara karanta wannan

ASUU Bata Da Wasu Dalilai Masu Kwari Na Ci Gaba Da Yajin Aiki - Buhari

Idan kana da manufa ko buri, hakan zai taimaka maka wajen sanin me ya kamata ka yi tare da mai da hankali ga abin da yafi dacewa,” a cewar Attajirin.

“Yin abin da aka saba da shi a rayuwar nan ba zai ba ka damar gano wata hanya sabuwa ba. Idan kuwa ka shiga naman wata hanya sabuwa, to tabbas za ka dace.”

Maduka
Cosmas Maduka: Attajirin Da Bai Taɓa Zuwa Makaranta Ba, Ko Talabijin Bai Da Shi
Asali: Facebook

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Sannan ya cigaba da cewa;

“Lokaci abu ne mai muhimmanci, akwai buƙatar ka san abin da ya kamace ka tun kana saurayi, da kuma tsara abin da kake fata ga rayuwarka.”

Sai dai mutane sun ƙara shan mamaki ne bayan da ya bayyana cewa shi fa takardar firamare ce kawai da shi, domin daga baya ne ya koyi yadda zai yi rubutu da karatu da Turanci.

Kara karanta wannan

Dan Achaba Ya Baje Kolin Dankareren Gidan Da Ya Ginawa Mai Shirin Zama Amaryarsa, Hoton Ya Ja Hankali

“Rayuwata aba ce da ke ƙushe cikin imani da yadda da ubangiji da kuma jajircewa,” a cewar Attajirin.

Har’ila yau, ya kuma bayyana cewa,

“Tun ina ƙarami na gano yadda nake so rayuwata ta kasance. A yau, ina lambar girmama wa da dakta har guda huɗu, da kuma ƙin karɓar wasu da dama. Hatta Najeriya ta san da zamana, sannan ana yin zaman taro na manyan hukumomi da ni; duk kuma ba tare da ilimin boko ba.”
“Don haka, ba na kallon talabijin kuma ban taɓa mallakar wani gidan talabijin ba. Sai dai an sha yin hira da ni a gidajen talabijin manya na duniya. Kuma na fara ne daga Naira 200 zuwa biliyoyin nairori a yanzu,”

Asali: Legit.ng

Authors:
AbdulRahman Rashida avatar

AbdulRahman Rashida