Yan Takarar Gwamna 837, ƴan Takarar Majalisa 10,240: INEC Ta Saki Sunayen Yan Takara
- A satin da ya gabata ne dai Hukumar Zaɓen ta bayar da Umarnin fara yakin neman zaɓen shugaban ƙasa da na ƴa. Majalissu
- Hukumar INEC ta saki jerin sunayen mutanen da aka tantance zasuyi takara a zabukan 2023
- A ƙalla ƴan Takara 13,000 da doriya ne zasu fafata a muƙamai da dama a zaben gwamna da majalisa
Legas - Akalla ‘yan takara 837 ne za su fafata a zaben gwamna da za a yi a ranar 11 ga Maris ɗin shekarar 2023 a jihohi 28, kamar yadda Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Kasa, INEC, ta sanar.
Shugaban hukumar ta INEC, Farfesa Mahmood Yakubu, ya bayyana hakan a taron kwararru kan dabarun gudanar da zaɓukan shekarar 2023 a jiya a jihar Legas, rahoton Vanguard.
Ya ce ƴan takara 10,240 ne kuma za su fafata a zaben ‘yan majalisar jiha yayin da ƴan takara 993 zasu fafata a zaɓen majalissar ƙasa.
An dai manna bayanan karshe na ƴan takarar a dukkan ofisoshin INEC na Jihohi a jiya, wanda hakan ya yi daidai da sashe na 32 (1) na dokar zabe ta 2022, wanda ta tanadi cewa za a fitar da jerin sunayen ‘yan takarar da da bayanan su akalla kwanaki 150 kafin babban zaɓe.
Za a gudanar da zabukan gwamnoni biyu a jihohin Kogi da Bayelsa nan gaba a wannan shekarar bayan gudanar da zaben a jihohin 28.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
INEC ta tabbatar wa ‘yan Najeriya kudirinta na inganta harkokin zabe da gudanar da mulki a kasa baki daya domin tabbatar da fara zaben 2023 a kan ƙari.
Idan Nayi Nasara Zan Sake Fasalin Najeriya Tare Habaka Tattalin Arziki Kasar, Kwankwaso Ya Yi Alkawari
Da yake jawabi a wurin taron kwararrun, Farfesa Yakubu ya ce
"maƙasudin taron shi ne duba irin kalubalen da ake fama da shi na tsawon shekara da shekaru da suka shafi tsarin zabe da yadda za a magance su.
“Hukumar ta kuduri aniyar inganta nasarorin da aka samu a zabukan baya-bayan nan da aka gudanar a jihohin Ekiti da Osun domin inganta yadda za a kai kayan zabe da kuma fara zaben tun da wuri.
“A dangane da haka, muna maraba da hadin gwiwa da Cibiyar 'Action Aid Nigeria' da kuma sauran ƙungiyoyin sa kai dan shirya wannan muhimmin taro da ya hada dukkan manyan ‘yan takara wuri guda domin tattaunawa kan muhimmin batutuwa.
"Hukumar ta kuduri aniyar ci gaba da inganta harkokinmu da tsarinmu domin baiwa 'yan Najeriya abun da suke buƙata"
Ya bayyana cewa ya zuwa yanzu hukumar ta samu nasarar aiwatar da ayyuka 9 cikin 14 dake jera a cikin jadawalin da aka tsara na babban zaben shekarar 2023.
“A yau (jiya kenan da yake jawabi ) za a buga jerin sunayen ‘yan takarar zaben Jihohi (Gwamnoni da na ‘yan Majalisun Jiha) a dukkan ofisoshinmu na kasa baki daya sannan a shigar da su a ƙundi yanar gizon hukumar kamar yadda doka ta tanada.", inji shi.
“A zaben gwamna da za a gudanar a jihohi 28 na tarayya, jam’iyyun siyasa 18 sun gabatar da jimillar ‘yan takara 837 da abokan takararsu. A mazaɓun Majalisar Jiha kuwa, ’yan takara 10,240 ne ke neman kujeru 993,”
Asali: Legit.ng