Kwankwaso: Rashin Aikin Yi Cikin Matasa Ka Iya Haifar da Tarzoma A Kasa
- Kwankwaso a yayin wata zantawa ya nuna damuwarsa ga rashin aikin yi da matasa ke fama da shi
- Sannan ya tabbatar da cewa rashin aikin yi ne musabbabin shaye-shaye da kuma ayyukan ta'addanci
- Ya kuma tabbatar da cewa muna na da tabbacin jam'iyyarsu za ta zama waraka ga al'umma
Jalingo - Ɗan takarar jami'yyar NNPP ya nuna damuwarsa game rashin ayyukan yi wanda ya nuna fargabar cewa hakan zai iya jawo rashin kwanciyar hankali a ƙasar.
Kwankwaso ya bayyana a hakan ne a cikin makon da ya gabata bayan wani taro na sirri da manyan jagororin jam'iyyar NNPP a garin Jalingo na jihar Taraba tare da ƙaddamar da ofishin jam'iyyar na jihar.
A cewarsa, rashin aiki a tsakanin matasa ya haifar da yawa sun rungumi shaye-shaye da kuma ayyukan ta'aadanci, rahoton Vanguard.
Idan Nayi Nasara Zan Sake Fasalin Najeriya Tare Habaka Tattalin Arziki Kasar, Kwankwaso Ya Yi Alkawari
Ɗan takarar ya yi alƙawarin dawo da martabar ƙasar idan aka zaɓe shi a zaɓen mai zuwa na shekarar 2023.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
A cewarsa, yana da ƙarfin guiwar sake farfaɗo da tattalin arzikin ƙasar da kuma samar da abubuwan more rayuwa wanda jin hakan ne ya sanya shi shiga takarar.
Har'ila yau, ya ce;
"ka ga, mu a tsarinmu shi ne cigaba da ƙyale mutane suna raina mu. Mu siyasarmu a zahiri take ba ta gangan ba ce. Mutane za su iya ganin magoya bayanmu kuma ƴan a-mutun-mu ne."
"Mutanen da suke mara mana baya, sun yi imanin cewa muna da gogewar da za mu iya samar da canji na gari kuma hakan zai inganta ƙasar nan. Wannan ne ya sa kake ganin mutane a ko'ina suna mara wa takararmu baya."
Haka kuma, Kwankwaso ya yi alƙawarin samar da gwamnatin da za ta ba wa kowa da kowa dama, idan aka zaɓe shugaban ƙasa a kakar siyasar 2023.
Ya kuma cigaba da cewa, a watannin baya, mutane da yawa na cike da kokwanton yiyuwar shigar jami'yyarmu harkokin zaɓen wanann shekara. Amma a yanzu komai na tunaninsu ya sauya.
"Watanni bakwai bayan a lokacin da muka yanke shawarar shiga wannan jam'iyya, mutane da yawa suna da tunanin ba za mu tsinana komai ba. Sai dai da taimakon Allah, yanzu kowa ya san mu," a cewar Kwankwaso.
Zan Sake Fasalin Najeriya Tare Habaka Tattalin Arzikin Kasar, Kwankwaso
A wani labarin kuwa, Sanata Rabi’u Kwankwaso, a ranar Litinin din nan data gabata, ya yi alkawarin habaka tattalin arzikin kasar tare da sake fasalin Nijeriya idan aka mara masa baya a zaben shekarar 2023
Kwankwason ya bayyana hakan ne lokacin da yake tattaunawa da manema labarai a Jalingo Babban birnin Jihar Taraba, ya kuma yi alkawarin sanya ilimi a matsayin farko a gwamnatinsa
Asali: Legit.ng