Allah Muke Roko Ya Bamu Mafi Alheri Tsakanin Atiku, Tinubu, Obi da Kwankwaso - Sarkin Hausawan Awka

Allah Muke Roko Ya Bamu Mafi Alheri Tsakanin Atiku, Tinubu, Obi da Kwankwaso - Sarkin Hausawan Awka

  • Ana ta samu ƙiraye-ƙiraye a tsakanin Shugabannin Al'umma kan wanda ya dace a zaba a 2023
  • Masu Zawarcin Shugabancin kasar nan na kara ƙaimi dan ganin sun sami magoya baya daga kowanne bangare na kasar nan
  • A ranar Larabar da ta gabata aka kaddamar da yakin neman zaben da zai gudana a Febrairu da Maris 2023

Sarkin al’ummar Hausawa, mazauna Amawbia da ke kusa da Awka, babban birnin jihar Anambra, Mahmud Sani ya bayyana cewa suna addu’ar Allah ya ba Najeriya shugaba mafi dacewa.

Mutum daya cikin manyan ‘yan takara hudu ake sa ran zasu lashe zaben 2023.

Sun hada Bola Tinubu na jam’iyyar APC; Atiku Abubakar na PDP da kuma Peter Obi na , LP da Rabiu Kwankwaso na NNPP.

Yan takara
Allah Muke Roko Ya Bamu Mafi Alheri Tsakanin Atiku, Tinubu, Obi da Kwankwaso - Sarkin Hausawan Awka
Asali: UGC

Ya ce

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Kara karanta wannan

Muhimmin Abun Da Zan Yi Idan Na Ɗare Kujerar Shugaban Ƙasa a Zaɓen 2023, Kwankwaso

"Hausawa mazauna jihar Anambra ba su da sha’awar nuna ƙabilanci ko banbancin addini, sai dai suna goyan bayan duk wani ɗan takara da zai iya sauya ragamar tare da maida da Nijeriya kan turba mikaƙƙiya."

Vanguard tace Sarkin wanda ya zanta da manema labarai a gidansa da ke Amawbia ya kara da cewa:

“A gare mu, ko dan kabilar Yaruba ko Bahaushe ko Igbo ya zama shugaban Najeriya a 2023, ba mu da haufi”.

Sarkin wanda ya gaji shugabancin al’ummar Hausawa daga mahaifinsa, ya yi waiwayen baya inda ya nuna yadda ɗan takarar shugaban kasa Obi, yai musu rijiyar burtsate a lokacin da yake Gwamnan Jihar Anambra wanda har yanzu suna ci gaba da amfana.

Ya kara da cewa, idan Obi zai iya samar da ababen more rayuwa ga kowa da kowa a matsayinsa na gwamna ba tare da nuna kabilanci ko addini ba, to haka na nuna zai iya bashi dammar yin aiyukan ci gaba a duk fadin kasar nan a matsayinsa na shugaban kasa ba tare da nuna kabilanci ko banbamcin addini ba.

Don haka ya yi addu’ar tare da fatan yin zabe cikin kwanciyar hankali a shekarar 2023, ya kuma bukaci Hausawa da su rika daukar yan kabilar Ndigbo a matsayin ‘yan’uwa, bisa kyakkyawar alakar da ke tsakaninsu, ba tare da la’akari da nuna wani bambanci ba.

Asali: Legit.ng

Authors:
AbdulRahman Rashida avatar

AbdulRahman Rashida