Matsalar Tsaro Zai Zama Tarihi Nan Ba Da Dadewa ba, Shugaba Buhari Ya Yiwa Yan Najeriya Alkawari
- Shugaba Buhari ya bada karfin gwiwan cewa nan ba da dadewa ba za'a shawo kan matsalar tsaro
- Buhari da gomman mukarrabansa na kasar Amurka don halartan taron gangamin majalisar dinkin duniya
- Buhari ya gabatar da nasa jawabin ga shugabannin duniya a taron ranar Laraba
Amurka - Shugaba Muhammadu Buhari ya bayyana cewa dubi da yadda dakarun sojin Najeriya suka kara kaimi wajen yakan yan bindiga, matsalar tsaro zai zama tarihi nan ba da dadewa ba.
Shugaban kasan ya bayyana hakan ne ranar Asabar a New York, birnin Amurka yayin zama da Firai Ministan kasar Ireland, Michel Martin.
A jawabin da mai magana da yawunsa, Femi Adesina, ya fitar ranar Asabar, yace:
"Shugaba Muhammadu Buhari a ranar Juma'a a New York ya bayyana cewa bisa yadda Sojojin Najeriya ke kokari, matsalar tsaro zata zama tarihi."
DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka
"Shugaba Buhari ya ce a watannin baya-bayan nan, kokarin da sojojin Najeriye keyi na nuna cewa muna hanyar shawo kan matsalar rashin tsaro."
"Zamu cigaba da had akai da kasashen duniya wajen amfani da fasaha saboda Najeriya ta amfana."
Adesina ya kara da cewa Firai Minista Mr Micheal Martin ya fadawa shugaba Buhari cewa kasar Ireland na neman hanyoyin karfafa alaka da Najeriya.
Ku Taimaka Ku Yafe Mana Basussukan Da Ake Binmu: Shugaba Buhari Ya Roki Shugabannin Duniya
A wani labarin kuwa, Shugaba Muhammadu Buhari ya yi kira da shugabannin kasashen duniya su yafewa Najeriya da kasashe masu tasowa basussukan da suke binsu saboda halin matsin tattalin arzikin da suke ciki.
A jawabin da yayi a taron gangamin majalisar dinkin duniya ranar Laraba, Buhari yace kasashe masu tasowa na fuskantar kalubale da dama, cike har da rashin iya bisa basussuka.
Ya bukaci shugabannin duniya su taimaka su sanya baki.
Asali: Legit.ng