Kashi 93% Na Yan Najeriya Na Da Hawan Jini, Kwararren Likititan Zuciya

Kashi 93% Na Yan Najeriya Na Da Hawan Jini, Kwararren Likititan Zuciya

  • Kungiyar Likitocin ciwon zuciya a Najeriya ta yaye sabbin masana harkar zuciya a Abuja
  • Shugaban kungiyar ya bayyana yadda hawan jini ya zama ruwan dare cikin mafi akasarin yan Najeriya
  • A cewarsa, abin ya fara shafan yara musamman a Arewa maso yamma da Arewa maso gabashin Najeriya

Shugaban kungiyar Likitocin Zuciya a Najeriya, Dr Okechukwu Ogah, ya bayyana yadda adadin masu ciwon zuciya yayi tashin gwauron zabo a Najeriya.

Yace kashi 93% na yan sama da shekaru 18 na da ciwon hawan jini a Najeriya.

Ogah ya bayyana hakan ranar Laraba a taron yaye sabbin mambobin kungiyar da aka yi a birnin tarayya Abuja, rahoton Leadership.

Yace hawan jini na daya daga cikin manyan abubuwan dake kawo ciwon zuciya da kuma rashin kula da kai.

Heaart
Kashi 93% Na Yan Najeriya Na Da Hawan Jini, Kwararren Likititan Zuciya
Asali: Getty Images

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Kara karanta wannan

Ba'a Taba Lalatacciyar Gwamnati Irinta Ta Buhari A Tarihin Najeriya Ba, Buba Galadima

Yace:

"Ciwon zuciya ya zama ruwan dare a Najeriya saboda irin rayuwa mara kyau da muke yi. Yanzu mutane da dama na fama da 'kiba, hawan jini da ciwon siga."
"Sama da kashi 24% na mutuwa a Najeriya sakamakon cututtukan zuciya ne."
"Muna da Likitocin zuciya 10,000 a Najeriya, wannan ya yi kadan kuma hakan na da hadari, muna fuskantar hijrar jami'an lafiya kuma idan ba'a dau mataki ba, wannan lamari zai munana."

A arewacin Najeriya kuwa, yace yanzu cikin kowani yaro 100 da aka haifa, daya na fama da ciwon zuciya.

Manyan Dalilai 7 Masu Hadari Zai Sa Kowa Ya Guji Cin Gandar Fatan Dabbobi

Yarbawa na kiransa 'Ponmo', Inyamurai kuma 'Kanda', Hausawa kuwa na cewa 'Ganda', fatar dabbobi na daga cikin abincin da 'yan Najeriya ke ci ba kakkautawa.

Gwamnati ta ce sam bai kamata jama'a suke cin wannan nau'in naman ba saboda yana rusa masana'antun fatu a kasar.

Kara karanta wannan

Gwamnan PDP: An kashe 'yan jiha ta 5000 cikin shekaru 11 a hare-haren 'yan bindiga

A 2019, hukumar kula da abinci da magunguna NAFDAC ta gargadi 'yan Najeriya game da cin ganda, inda tace yana da matsala ga lafiya.

Asali: Legit.ng

Online view pixel