Kada Kuyi Asarar Kuri'unku, Kada Ku Zabi Musulmai: Yakubu Dogara Ga Kiristoci
- Hanarabul Yakubu Dogara ya caccaki jam'iyyarsa ta APC kan zaben Shettima matsayin abokin tafiyar Tinubu
- Dogara ya yi kira ga mabiya addinin Kirista kada suyi asarar kuri'unsu saboda Ubangiji bai son asara
- Kungiyar Kiristocin Najeriya CAN ta bayyana cewa har abada ba zata amince da tikitin Tinubu ba
Abuja - Tsohon Kakakin majalisar wakilan tarayya, Yakubu Dogara, ya bayyana cewa tikitin Musulmi da Musulmi da jam'iyyar All Progressives Congress, APC, tayi zai kare a abin kunya.
Dogara ya bayyana hakan a taron da Gamayyar kiristocin Najeriya watau 'Nigerian National Christian Coalition' ta shirya.
Ya caccaki jam'iyyarsa ta APC inda yace sai da suka yi gargadi kada a zabi Shettima amma aka yi.
Yace:
"A nasu tunanin, sun zabi gina kai maimakon gina kasa; abinda ba'a taba yi ba a tarihi kuma bamu bukatan boka ya fada mana a kunya zasu kare."
"Na yi farin ciki sosai Kiristocin Najeriya sun tashi tsaye don magana kan abinda wasu jam'iyyu suka yi."
DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka
Tsohon Kakakin majalisan ya yi kira ga Kiristoci kada su sake suyi asarar kuri'unsu a zaben 2023.
Yace:
"Duk Kirista ya sani cewa Ubangiji bai son asara. Ba halin Kirista ne Coci tayi asarar damar da aka bamu."
"Na yi iyakan kokari ne wajen tabbatar da cewa kada kiristoci suyi asarar kuri'unsu."
Dogara yace tun kafin zaben Shettima, kiristoci sun gargadi APC amma a banza.
Shugabannin Kiristoci Sun Shirya Zama Da Dukkan Yan Takara Kujeran Shugaban Kasa
Mun kawo muku cewa Gabanin zaben 2023, gamayyar shugabannin kiristocin Najeriya tace tana shirya zama da duk dan takarar kujeran shugaban kasan dake son cin zabe, rahoton Punch.
Gamayyar ta Nigerian National Christian Coalition ta bayyana cewa duk dan takaran da yaki zama da shugabannin Kirista ba zai ci zabe ba.
Ana shirya zaman ne tsakanin shugabannin Coci da yan siyasa domin gabatar musu da bukatun mabiya addinin Kirista don sanin wanda zai yi da su, cewarta Titi.
An shirya zaman ranar 20 ga Satumba, 2022 a farfajiyar International Conference Centre, dake birnin tarayya Abuja.
Asali: Legit.ng