Taron Gangamin UN: Hotuna da Bidiyon Shugaba Buhari Yayinda Ya Dira Birnin New York

Taron Gangamin UN: Hotuna da Bidiyon Shugaba Buhari Yayinda Ya Dira Birnin New York

Shugaba Muhammadu Buhari ya isa birnin New York, kasar Amruka don halartan taron gangamin majalisar dinkin duniya.

Wakilin kamfanin dillancin labaran Najeriya NAN ya ruwaito cewa Shugaba Buhari ya dira babbar tashar jirgin JF Kennedy ne misalin karfe 6:20 na yamma.

Shugaban kasan ya samu tarba daga wajen Ministan harkokin wajen Najeriya, Geoffrey Onyeama; wakilin Najeriya a majalisar dinkin duniya, Tijjani Muhammad-Bande da jakadan Najeriya zuwa Amurka, Dr Mrs Uzoma Emenike, dss.

A cewar rahoton Vanguard, Shugaba Buhari zai gabatar da jawabin farko na ranar Laraba.

Zai gabatar da jawabinsa misalin karfe 2 na rana (agogon Najeriya)

Hakazalika zai halarci zaman kwamitin shugabannin kasashen Afrika kan sauyin yanayi da kiwon lafiya.

Kalli hotunan:

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Kara karanta wannan

Jerin Gwamnoni, Ministoci, Shugabannin hukuma Kimanin 20 Da Suka Yiwa Buhari Rakiya Amurka

buhari arrive
Taron Gangamin UN: Shugaba Buhari Ya Dira Birnin New York Hoto: Buhari Sallau
Asali: Facebook

Hoto: Buhari Sallau

Kallo bidiyon:

Asali: Legit.ng

Authors:
AbdulRahman Rashida avatar

AbdulRahman Rashida

Tags: