Shugaba Buhari Zai Tafi Amurka Halartan Taron UN Gobe Lahadi

Shugaba Buhari Zai Tafi Amurka Halartan Taron UN Gobe Lahadi

  • Shugaban kasa Najeriya, Muhammadu Buhari, zai halarci taron ganganmin majalisar dinkin duniya
  • Shugaban kasan zai samu rakiyar uwargidarsa, Aisha Buhari, wasu gwamnoni, ministoci da manyan jami'an gwamnati.
  • Shugaban Bihari zai yi mako guda daya a Amurka kuma ya dawo kasar ranar Litnin, 26 ga Satumba

Abuja - Shugaba Muhammadu Buhari zai tafi birnin New York kasar Amurka ranar Lahadi, 18 ga watan Satumba, don halartan taron gangamin majalisar dinkin duniya (UNGA77).

A bisa jawabin da Mai magana da yawun shugaban kasa, Femi Adesina, ya fitar ranar Asabar, tuni an fara shirye-shiryen taron gangamin, rahoton AriseTV.

Ya bayyana cewa abubuwan da za'a tattauna a taron gangamin sun hada da rikicin Rasha da Ukraine, sauyin yanayi, annobar Korona, da makamashi.

Shugaba Buhari zai gabatar da nasa jawabin ranar Laraba, 21 ga Satumba, 2022.

Kara karanta wannan

Jam'iyyar PDP Ba Ta Dan Takaran Gwamna a Zaben 2023, Kotu Ta Soke Zaben Fidda Gwani

BUhari
Shugaba Buhari Zai Tafi Amurka Halartan Taron UN Gobe Lahadi Hoto: Presidency
Asali: Facebook

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Bayan jawabin, Adesina yace Buhari zai halarci wasu taruka da ganawar diflomasiyya da shugabannin duniya, yan kasuwar, da kungiyoyi.

Shugaban kasan zai samu rakiyar uwargidarsa, Aisha Buhari, wasu gwamnoni, ministoci da manyan jami'an gwamnati.

Ya ce Shugaban kasa zai dawo kasar ranar Litnin, 26 ga Satumba.

Asali: Legit.ng

Authors:
AbdulRahman Rashida avatar

AbdulRahman Rashida