Wannan Bai Dace Ba: Gwamnatin Rasha Ta Nuna Baci Rai Kan Rashin Gayyatarta Jana'izar Elizabeth

Wannan Bai Dace Ba: Gwamnatin Rasha Ta Nuna Baci Rai Kan Rashin Gayyatarta Jana'izar Elizabeth

  • Jami'an ma'aikatar diflomasiyyan kasar Rasha sun ce rashin gayyatarsu jana'izar Sarauniya Elizabeth bai dace ba
  • Gwamnatin ta Rasha tace ofishin jakadancin Birtaniya ta aike mata da sakon daliln rashin gayyatarsu
  • Masarauta da gwamnatin kasar Ingila ta sanar da cewa za'a yi jana'izar Sarauniyar Elizabeth II ranar Litinin 19 ga watan Satumba, 2022

Gwamnatin kasar Rasha ta caccaki gwamnatin Birtaniya kan rashin gayyatar jami'anta jana'izar Sarauniya Elizabeth II, tace wannan rashin kyautatawa ne.

Kakakin ma'aikatar harkokin wajen kasar Rasha, Maria Zakharova, a ranar Juma'a ya ce gwamnatin Birtaniya tace da an ki gayyatar Rasha ne saboda yakin da wakana a kasar Ukraine.

Rasha
Wannan Bai Dace Ba: Gwamnatin Rasha Ta Nuna Baci Rai Kan Rashin Gayyatarta Jana'izar Elizabeth Hoto: Kremlin
Asali: Facebook

A jawabin Maria Zakharova, ya tuhumci Birtaniya da nuna son kai da goyawa Ukraine baya, rahoton NAN.

A cewarsa:

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Kara karanta wannan

2023: Tsohon Kakakin Majalisar Tarayya, Ghali Na'Abba, Ya Sauya Sheka Zuwa PDP, Ya Fallasa Sirrin APC

"A ra'ayinmu ana son amfani da matsalar da ta shafi kowa wajen cimma wata mafita ta fito-na-fito da kasarmu kuma wannan rashin hallaci ne."
"Elizabeth II babbar mutum ce kuma bata yi katsalandan cikin harkokin siyasa ba, amma hakan bai hana gwamnatin Birtaniya sakin jawabin raba kan mutane ba."

Jerin Shugabanni 3 Da Aka Ki Gayyata Taron Jana'izar Sarauniya Elizabeth

Masarauta da gwamnatin kasar Ingila sun sanar da cewa za'a yi jana'izar Sarauniyar Elizabeth II ranar Litinin 19 ga watan Satumba, 2022 a birnin Landan.

Sashen Hausa na BBC ta ruwaito cewa a karshen makon da ya gabata an aika takardun gayyatar zuwa jana'izar ga shugabanni da sarakuna da sauran manyan mutane a fadin duniya,

Rahoton ya kara da cewa akalla shugabannin kasashe da manyan mutane fiye da 500 ake kyautata zaton za su halarci jana'izar.

Za a yi taron a babban dakin Westminster Abbey daukar mutum 2,200.

Kara karanta wannan

Jerin Shugabanni 6 Da Aka Ki Gayyata Taron Jana'izar Sarauniya Elizabeth Da Dalili

Amma akwai wasu shugabannin kasashe uku da ba'a aikewa takardar gayyata ba,a cewar wakilin BBC James Landale

Jerin Shugabanni 3 Da Aka Ki Gayyata Taron Jana'izar Sarauniya ElizabethJerin Shugabanni 3 Da Aka Ki Gayyata Taron Jana'izar Sarauniya Elizabeth

Asali: Legit.ng

Authors:
AbdulRahman Rashida avatar

AbdulRahman Rashida