Kano: Jami'an NSCDC an Kama Matashi Ya Kuntuka Sata a Masallaci
- Jami'an hukumar NSCDC dake jihar Kano sun cafke wani matashi mai shekaru 22 kan zargin sata a Masallaci
- Zaharadeen Mukhtar mai shekaru 22 ya kwashe tagogin karfe na babban Masallacin Juma'a dake Dawakin Tofa
- An kama shi da kayayyakin satan a wani babban buhu yayin da ya garzaya kasuwa domin siyar da su
Kano - Jami'an hukumar Nigerian Security and Civil Defence Corps (NSCDC), reshen jihar Kano, sun damke wani matashi mai shekaru 22 mai suna Zaharadeen Mukhtar kan zarginsa da barna da satar tagogin babban Masallacin Dawakin Tofa dake jihar.
DSC Ibrahim Idris Abdullahi, mai magana da yawun reshen, ya bayyana hakan a takardar da ya fitar a ranar 14 Satumba.
Yace Mukhtar mazaunin kauyen Kashirmu a karamar hukumar Dawakin Tofa an kama shi ne bayan ya sace kayayyaki tare da boye su a wani babban buhu tare da kai su kasuwa.
"Wanda ake zargin tuni ya amsa laifukansa kuma za a mika shi gaban kuliya bayan an kammala bincike."
DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar
- Yace.
NDLEA Tayi Ram da Mai Tsohon Ciki Dauke da Miyagun Kwayoyi
A wani labari na daban, hukumar yaki da fasa-kwabrin miyagun kwayoyi, NDLEA, ta damke wata mata mai tsohon ciki mai shekaru 25 dauke da kwayoyin methamphetamine a garin Auchi dake jihar Edo.
Kakakin NDLEA, Femi Babafemi, ya sanar da hakan a wata takarda da ya fitar a Abuja ranar Lahadi.
Babafemi yace wacce ake zargin mai suna Haruna Favour, wacce aka kama ranar Juma'a, an kama ta dauke da nau'ikan wiwi da magungunan ruwa masu dauke da codeine.
Yace yunkurin da wasu dillalan kwayoyi suka yi na fitar na 7.805kg na methamphetamine zuwa Amurka da Australia, ya watse bayan jami'an NDLEA sun bankado hakan a Legas.
Asali: Legit.ng