Duk Karyace Muke Yiwa Mutane, Auren Mace Fiye Da Daya Halas Ne: Rabaran Fada Ya Bayyana Yayinda Yayi Murabus

Duk Karyace Muke Yiwa Mutane, Auren Mace Fiye Da Daya Halas Ne: Rabaran Fada Ya Bayyana Yayinda Yayi Murabus

  • Mun Dade muna boyewa jama'armu gaskiya, Aure Mata Fiye Da 1 Halas Ne, Cewar Rabaran Fada
  • Malamin addinin Kiristan ya yi murabus daga kujerarsa ta babban Bishop a cocin Anglican dake Nnewi
  • Fada Ogbuchukwu ya yi kira ga Maza su auri 'yan matan da suke lalata da su don kada su shiga wuta rana gobe Kiyama

Anambra - Wani babban Bishop na cocin Anglican dake Nnewi jihar Anambra, Rabaran Fada Ogbuchukwu Lotanna, ya yi murabus daga kujerarsa a Cocin.

Rabaran Fada Lotanna, a jawabin murabus dinsa yace ya samu sabon umurni na ya kwadaitar da mutane kan auren mace fiye da daya don a rage zinace-zinace cikin al'umma, rahoton Punch.

A cewarsa, auren mace fiye da guda ba haramun bane sabanin abinda ake tunani.

Yace Ubangiji na son mutane su auri mata fiye da daya maimakon neman matan aure da yan mata.

Kara karanta wannan

Shirin Karin Albashi: Naira Milyan Daya Muke Biyan yan majalisa da Ministoci Albashi A Wata, Gwamnatin Tarayya

Yace Coci ta dade tana boye hakan ga mambobinta kuma lokaci ya yi da za'a fadawa mutane gaskiya.

Ya yi kira ga Maza su auri 'yan matan da suke lalata dasu don kada su shiga wuta rana gobe Kiyama, riwayar TheNation.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Rabaran
Duk Karyace Muke Yiwa Mutane, Auren Mace Fiye Da Daya Halas Ne: Rabaran Fada Ya Bayyana Yayinda Yayi Murabus Hoto: PMNews
Asali: Facebook

Ya ce zai kafa sabuwar cocinsa mai suna "Gideonites”.

A cewarsa:

"Ko shakka babu cocina musamman na Anglican sun dade suna haramtawa mutane auren mace fiya da guda, amma Ubangiji ya bude idona kuma na fahimci gaskiya hakan ba laifi bane."

Har yanzu cocin Anglican na Nnewi bata yi tsokaci kan murabus din Fada Lotanna ba.

Ku Kama Mazajenku Da Kyau, Maza Tsada Suke

A wani labarin kuwa, wata matashiya yar Najeriya da ke zama a kasar waje ta yi bidiyo a TikTok, tana mai shawartan yan matan Najeriya a kan kada su zo Birtaniya da tunanin samun miji.

Kara karanta wannan

Sai Ta An yi Addu'a, Ubangiji Bai Fada Min Za'a Yi Zabe A 2023 Ba, Fasto Enoch Adeboye

Ta bayyana cewa a UK, aiki shine mazajensu. Budurwar ta shawarci yan matan da ke Najeriya a kan su rike mazajensu da kyau.

Asali: Legit.ng

Authors:
AbdulRahman Rashida avatar

AbdulRahman Rashida