Wakokin Sabawa Koyawar Addini Da Al'adu: Jerin Sunayen Mutum 10 Da Kotun Kano Tayi Umurnin A Bincika

Wakokin Sabawa Koyawar Addini Da Al'adu: Jerin Sunayen Mutum 10 Da Kotun Kano Tayi Umurnin A Bincika

Babbar kotun shari'a dake zamanta a karamar hukumar Bichi karkashin jagorancin Dr Bello Musa Khalid ta umurci hukumar yan sanda ta damke wasu mutum 10 kuma ta bincikesu kan wasu wakoki da bidiyoyi da suka yi.

Wannan ya biyo bayan shigar da su kara da Barista Badamasi Suleiman Gandu da wasu lauyoyi biyar mazauna Kano sukayi, rahoton DailyTrust.

Sun zargi mawakan da yada alfasha, fasadi da rashin tarbiya kuma hakan ya sabawa koyarwar addini da al'adun jihar Kano.

GWanja
Wakokin Sabawa Koyawar Addini Da Al'adu: Jerin Sunayen Mutum 10 Da Kotun Kano Tayi Umurnin A Bincika Hoto: NBC
Asali: UGC

Ga jerin sunayen mutum 10 da aka shigar kotu

1. Ado Gwanja

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

2. Mr 442

3. Safarau

4. Dan Maraya

5. Amude Booth

Kara karanta wannan

Kwanaki 9 Da Bada Umurnin Damke Ado Gwanja, Safarau Da Yan TikTok 8, Har Yau Ba'a Kamasu Ba

6. Kawu Dan Sarkim

7. Murja Ibrahim Kunya

8. Ummi Shakira

9. Samha M. Inuwa

10. Babiyana.

Kwanaki 9 Da Bada Umurnin Damke Ado Gwanja, Safarau Da Yan TikTok 8, Har Yau Ba'a Kamasu Ba

Kotun ta bada umurnin ne tun ranar Talatar makon jiya, jami'in kotun Baba-Jibo Ibrahim ya bayyana hakan.

A cewar Baba-Jibo:

"Kotun Shari'ar ta bada umurni ga kwamishanan yan sanda ya damke wadannan mutum 10 kuma a gudanar da bincike kan rawar da suka taka wajen bayyanawa rashin tarbiyya."

Ana zargin Ado Gwanja da sakin waka mai suna "A Sosa".

Amma kwanaki tara bayan da kotu ta bada wannan umurnin, har yanzu ba'a damkesu ba, Ibrahim yace.

A cewarsa:

"Zamu jira kammaluwar binciken da yan sanda ke yi domin sanin matakin da kotu zata dauka."

Asali: Legit.ng

Authors:
AbdulRahman Rashida avatar

AbdulRahman Rashida