An Gano Wani Yaro Da Ya Boye Cikin Jirgi, Yace Ya Gaji Da Najeriya

An Gano Wani Yaro Da Ya Boye Cikin Jirgi, Yace Ya Gaji Da Najeriya

  • Wani yaro ya shiga tashar jirgin saman Murtala dake Legas ta barauniyar hanya har ya samu shiga cikin jirgi
  • Yaron dan kasa da shekaru 15 ya ce ya gaji da zaman Najeriya shi yasa yake son bin masu zuwa kasar waje
  • Jami'an kamfanin jirgin saman suka ganoshi cikin jirgi bayan ya fadi sumamme

Lagos - An gano wani dan shekara 14 sumamme cikin jirgin kamfanin United Nigeria inda ya boye yana jiran jirgin ya tashi da shi inda zai yi tafiya kasar waje.

Jami'in yada labaran tashar jirgin Murtala MMA2 dake Legas ya bayyana cewa yaron ya bada labarin yadda ya samu shiga tashar jirgin ta katangar dake titin Lagos-Abeokuta, rahoton Tribune.

Yaron mai suna Rasheed Muftau, yace ya gaji da Najeriya saboda haka yana son fita kasar waje.

Kara karanta wannan

Wani Matashi Ya Koma Jami'ar Da Yayi Karatu, Yace Su Bashi Kudinsa Su Karbi Kwalinsu

MMA22
An Gano Wani Yaro Da Ya Boye Cikin Jirgi, Yace Ya Gaji Da Najeriya

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

A cewar Onalaja:

"Misalin karfe 6:10 na safiyar Lahadi, 4 ga Satumba 2022, Kamfanin jirgin United Nigeria ya sanar da Bi-Courtney Aviation Services Ltd (BASL) cewa an tsinci wani dan shekara 14 cikin daya daga cikin jiragensu."
"An fito da yaron daga cikin jirgin kuma aka kaishi asibitin MMA2. Daga baya aka kaishi asibitin FAAN inda ya farfado misalin karfe 10:20 na safe."
Yaron ya bayyana cewa shi maraya ne kuma ya samu shiga tashar jirgin ta wani budaddiyar kofa a Ile-Zik, titin Lagos-Abeokuta."
"Yaron yace niyyarsa itace yin tafiya, saboda ya gaji da kasar nan."

Kamfanin Bi-Courtneu ya bayyana cewa tuni an sallami yaron daga asibiti kuma an kaishi ofishin masu laifi na FAAN dake tashar jirgin Murtala Mohammed.

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel