Jerin Sabbin Kadarorin Abba Kyari 14 Da Gwamnati Ta Bankado

Jerin Sabbin Kadarorin Abba Kyari 14 Da Gwamnati Ta Bankado

Mun kawo muku labarin cewa gwamnatin tarayya ta gano wasu kadarori 14 wanda ake zargin Abba Kyari ya mallaka na filaye, gidaje da makudan kudade.

Ofishin Ministan shari’a kuma babban Lauyan gwamnatin Najeriya yana zargin DCP Kyari da laifin boye gaskiya a game da mallakar wadannan dukiyoyi.

Tun tuni dai ake shari’a da babban jami’in ‘dan sandan.

An shigar da karar mai lamba FHC/ABJ/CR/408/22 a kotun tarayya na garin Abuja. Mohammed Kyari da Ali Kyari suna cikin wadanda za su amsa laifi.

Abba Kyari
Jerin Sabbin Kadarorin Abba Kyari 14 Da Gwamnati Ta Bankado Hoto: DCP Abba Kyari
Asali: UGC

Legit ta tattaro muku jerin wadannan kadarori 14

1. Fuloti mai lamba 1927 Blue Fountain Estate, Karsana, Abuja

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

2. Rukunin Gidaje a Linda Chaulker Road, Asokoro Extension; Abuja

Kara karanta wannan

Layin Fetur Na Shirin Dawowa, ‘Yan Kasuwa Sun Tafi Yajin-aiki Saboda Bashin N50bn

3. Fuloti na 5 mai lamba BO/4546 a Maiduguri

4. Fuloti na 9 mai lamba BO/1037 a Maiduguri

5. Fuloti na 10 mai lamba CER/4319 a Maiduguri

6. Fuloti na 33 mai lamba BO/4319, a Maiduguri

7. Kantin Shaguna dake number 4, Aliyu Close hanyar Giwa Barracks, Maiduguri

8. Filin Polo plot no. 270, Maiduguri

9. Gidan Gona a hanyar Abuja-Kaduna

10. Plaza da ake kan ginawa a Guzape, Abuja

11. Є17,598 bankin GTB

12. N2.9 million a UBA

13. N366, 258.77 a Sterling Bank

14. N88,000 a Sterling Bank.

An fara shari'ar Abba Kyari kan safarar miyagun kwayoyi, NDLEA ta gabatar da shaida

Hukumar hana sha da fataucin miyagun kwayoyi ta ƙasa NDLEA ta buɗe shari'a da dakataccen mataimakin kwamishinan yan sanda, DCP Abba Kyari kan tuhumar safarar miyagun kwayoyi a babbar kotun tarayya, Abuja.

Hukumar ta gabatar da kwamandan miyagun kwayoyi (sashin bincike), Patricia Afolabi, domin ta ba da shaida ta farko a gaban mai shari'a Emeka Nwitw, kamar yadda jaridar Punch ta ruwaito.

Shaidar ta faɗa wa Kotu cewa aikinta a hukumar NDLEA ya ƙunshi karba da kuma gudanar da bincike kan abubuwan da suka shafi miyagun kwayoyi.

Asali: Legit.ng

Authors:
AbdulRahman Rashida avatar

AbdulRahman Rashida