Da duminsa: Dan Takaran Gwamnan Jihar Ogun Na Jam'iyyar PRP Ya Mutu Kwana 6 Bayan Shiga

Da duminsa: Dan Takaran Gwamnan Jihar Ogun Na Jam'iyyar PRP Ya Mutu Kwana 6 Bayan Shiga

  • Kwanaki shida kacal bayan shiga takarar neman kujerar gwamna, Farfesa Bangbose ya mutu
  • Dan siyasan ya kwanta dama ne bayan rashin lafiyar da yayi gajeruwar jinya a garin Abeokuta
  • Kwanakin baya Bamgbose ya fita daga jam'iyyar PDP saboda an kwace tikitin takarar kujerar Sanata daga hannunsa

Abeokuta - Dan takaran kujerar gwamnan jihar Ogun karkashin jam'iyyar Peoples Redemption Party PRP, Farfesa David Bamgbose, ya rigamu gidan gaskiya.

Dan takaran ya mutu ne kwanaki shida kacal bayan alanta niyyar takara.

Punch ta ruwaito cewa Bamgbose ya mutu ne a asibitin Sacred Heart hospital, Lantoro, Abeokuta, bayan gajeruwar jinya.

Hadiminsa na jiki, Mr Oduntan Olayemi, ya tabbatar da mutuwarsa.

DOB 4
Da duminsa: Dan Takaran Gwamnan Jihar Ogun Na Jam'iyyar PRP Ya Mutu Kwana 6 Bayan Shiga Hoto: dailytrust.com
Asali: UGC

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Ya yi bayanin cewa gajiya kawai dan siyasan yace yana ji sai aka kaishi asibiti, kuma daga baya aka bukaci a garzaya dashi FMC Abeokuta.

Kara karanta wannan

Bidiyo: Bindiga Ta Ki Tashi Yayinda Wani Yayi Kokarin Kashe Mataimakiyar Shugaban Kasar Argentina

Daga baya aka kaishi Lantoro inda aka sa miki na'urar numfashi (oxygen) har ya mutu ranar Juma'a.

A cewarsa:

"Jiya yake mana korafin ya gaji sai muka yanke shawarar kaishi asibitin dake Olomore. Sai aka ce mu tafi FMC don wasu gwaje-gwaje."
"Sai muka zabi asibitin jiha dake Lantoro saboda jikin yayi tsanani kuma aka bashi gado inda aka sanya masa Oxygen har yau."
"Da safen nan na koma asibitin na sameshi yana numfashi mai nauyi. Na je sayo masa magani da Likita yayi umurni na samu labarin ya mutu."

Farfesa Bamgbose ya bar mata gida, Mary Bamgbose da 'yaya shida.

Kwanakin baya Bamgbose ya sauya sheka daga jam'iyyar Peoples Democratic Party PDP saboda an kwace tikitin takarar kujerar Sanata daga hannunsa.

Mataimakin Shugaban PDP Ya Fice Daga Jam’iyya, Ya Aikawa Iyochia Ayu Wasikarsa

A wani labarin, Hon. Leye Odunjo ya sauka daga matsayinsa na mataimakin shugaban jam’iyyar PDP na reshen jihar Ogun.

Kara karanta wannan

2023: Wani Babban Jigon APC da Dubbannin Magoya Baya Sun Sauya Sheka Zuwa PDP

The Nation ta fitar da rahoto a ranar Alhamis, 1 ga watan Satumba 2022, tace Hon. Leye Odunjo ya bada sanarwar ficewarsa daga jam’iyyar PDP.

Tsohon ‘dan majalisar ya shaidawa Duniya ya yi murabus ne a wata wasika da ya aikawa shugaban jam’iyyar PDP na kasa, Sanata Iyorchia Ayu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel