Hukumar EFCC Ta Kama 'Yahoo Boys' 41 Da Dukiyoyin Da Suka Mallaka
- Yau kamar kullum, jami'an hukumar EFCC sun kai samame gidajen matasan 'Yahoo-Yahoo Boys'
- An samu nasarar tattara sama da matasan arba'in tare da dukiyoyin da suka mallaka a Awka
- Matasan Najeriya yanzu da dama sun shiga sabuwar harkar damfara da sata ta hanyar yanar gizo
Hukumar hana almundahana da yiwa tattalin arzikin kasa zagon kasa watau EFC ta cika hannu da yan damfarar yanar gizo wanda aka fi sani da Yahoo Boys 41.
Matasan 'Yahoo Boy' sun shahara da sace kudaden mutane ta manhajojin bankin wayansu da kuma yanar gizo.
EFCC ta bayyana hakan ne a jawabin da ta fitar ranar Juma'a, 2 ga watan Satumba, 2022.
Hukumar tace:
"Hukumar EFCC shiyyar Enugu ta sami nasarar kama wasu mutane arba’in da daya da take zargi da zamba ta yanar gizo a garin Awka na jihar Enugu.
Hukumar ta kama su ne bayan samun wasu bayanan sirri da ta samu game da ayyukan da suke aikatawa.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Goma sha shida daga cikinsu an kama sune a titin Umuodu Tansi dake Awka, jihar ta Anambra sai kuma sauran ashirin da biyar da aka kama a kauyen Umudu Okpuno karamar hukumar Akwata kudu duk a jihar ta Anambra."
Wadanda aka kama Sun hada da: Eze Stanley Chineze, Emmanuel Chijioke Ejikeme, Chinonso Edwin Abonyi, Emmanuel Akoi Chibuike, Henry Umenyi Chukwualuka, Ayo Iteze Chidiebere, Emeka Justice, Emmanuel Ayakem, Ememuo Innocent Ifeanyi da Odinaka Udeh.
Sauran sune: Okonkwo Stanley Chukwuma, Ezeakolam Godswill Chihurumnanya, Emmanuel Mgbakor kenechukwu, Benneth Odinaka, Ndefor Chukwudi, Ngadi Chima, Akalam Lucky Ibuchi, Akalam Michael, Justus Akalam Chunazom, Akalam Kenneth , David Monday Ebuka, Uchechukwu Kingsley Ebuka, Henry Echezona, Onyedika Chukwu, Abuchi Awa, Henry Adumaka, Chidera Chika, Malachi Asonbe, Cosmos Obidimma da Akuma Wisdom.
Sai kuma: Agwu Victor, Godwin Okoro, Obumneke Nwankwo, Igboanugo Charles, Ibeh Chisom, Agbafuna Ifeanyi, Chukwu Joseph, Chukwu Benard, Anson Ugochukwu, Mathew Chukwuemeka da Temple Emmanuel.
An kama su da wayoyi da kwamfiyutoci da motoci, sannan za’a gurfanar dasu gaban kotu bayan an kammala bincike.
Asali: Legit.ng