Jami'ar Nasarawa Za Tayi Watsi da ASUU Yayinda Gwamna Yayi Alkawarin Biyansu Albashinsu

Jami'ar Nasarawa Za Tayi Watsi da ASUU Yayinda Gwamna Yayi Alkawarin Biyansu Albashinsu

  • Jami'ar jihar Nasarawa za ta shiga jerin jami'o'in da zasuyi watsi da yajin aikin Malaman jami'a ASUU
  • Gwamnan jihar Nasarawa ya yi alkawarin fara biyan ma'aikatan jami'ar albashi daga asusun gwamnati
  • Alamu sun bayyana cewa gwamnatin tarayya na shirin bude jami'o'in Najeriya duk da yajin aikin ASUU

ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit

Lafia - Da alamun za'a koma karatu jami'ar Nasarawa State University Keffi (NSUK) bayan gwamnatin jihar ta yi alkawarin fara biyansu albashinsu daga baitul mali.

Gwamnan jihar Nasarawa, Injiniya Abdullahi Sule, ya bayyana hakan yayin zaman majalisar zartaswa jihar ranar Labara a gidan gwamnatin jihar.

Injiniya Sule yace sun yanke shawarar daukar nauyin biyan albashin Malaman ASUU saboda haka zasu koma aji, rahoton ChannelsTV.

A cewar gwamnan, gwamnatin zata fara biyan albashin Malaman fari daga watan nan.

Kara karanta wannan

Karin Bayani: Mai Magana da Yawun Rundunar 'Yan Sanda a Najeriya Ya Mutu

NSUK Keffi
Jami'ar Nasarawa Za Tayi Watsi da ASUU Yayinda Gwamna Yayi Alkawarin Biyansu Albashinsu Hoto: NSUK
Asali: Facebook

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ya kara da cewa shugabannin jami'ar, kungiyar ma'aikatan SSANU da NASU duk sunyi alkawarin komawa bakin aiki.

Yace:

"Daya daga cikin sharrudan da suka bamu shine mu dau nauyin biyan albashin dukkan ma'aikatan jami'ar, saboda su daina amfani da kudin shigarsu."
"Da muka duba baitul malinmu, mun ga akwai isasshen kudi kuma saboda muhimmancin da muka ba ilimi, zamu fara biya daga wannan watan."
"Kuma muna kyautata zaton cewa idan muka biyasu ranar Alhamis ko Juma'a, zasu koma aji."

Jami'ar IBB Dake Lapai Jihar Neja Ta Janye Daga Yajin Aikin ASUU, Tace Dalibai Su Koma Aji

A wani labarin kuwa, jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida dake garin Lapai, jihar Neja ta sanar da daukacin dalibai da Malamai su gaggauta komawa aji ba tare da bata lokacin.

Kwamitin Shugabannin makarantar ta bayyana hakan ne a jawabin da mataimakin Rajistran ya fitar ranar Talata, 30 ga watan Agusta, 2022.

Kara karanta wannan

Gwamnatin Tarayya Na Shawarar Bude Jami'o'i Duk Da Yajin Aikin ASUU

Ya bayyana cewa sun yanke shawarar haka bayan zaman da majalisar zartaswa na jam'iyar tayi ranar Talata.

Asali: Legit.ng

Authors:
AbdulRahman Rashida avatar

AbdulRahman Rashida