Jami'ar IBB Dake Lapai Jihar Neja Ta Janye Daga Yajin Aikin ASUU, Tace Dalibai Su Koma Aji
- Jami'ar IBBUL ta shiga jerin jami'o'in da suka yiwa kungiyar Malamai ta ASUU bore kan yajin aiki
- Shugabannin jami'ar sun umurci dalibai su koma aji daga ranar Litnin, 5 ga Satumba, 2022
- Alamu sun bayyana cewa gwamnatin tarayya na shirin bude jami'o'in Najeriya duk da yajin aikin ASUU
Neja - Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida dake garin Lapai, jihar Neja ta sanar da daukacin dalibai da Malamai su gaggauta komawa aji ba tare da bata lokacin.
Kwamitin Shugabannin makarantar ta bayyana hakan ne a jawabin da mataimakin Rajistran ya fitar ranar Talata, 30 ga watan Agusta, 2022.
Ya bayyana cewa sun yanke shawarar haka bayan zaman da majalisar zartaswa na jam'iyar tayi ranar Talata.
Mataimakin Rajistar, Alhaji Baba Akote, yace:
"Muna sanar da dukkan ma'aikata da daliban jami'ar Ibrahim Badamasi,Lapai cewa za'a kara karatun zango na biyu 2020/2021 daga ranar Litinin, 5 ga watan Satumba, 2022."
"Majalisar zartaswar jami'ar ta bayyana wannan umurni ne bayan zamanta na 55 da akayi ranar Talata, 30 ga Agusta, 2022."
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
"Hakazalika ana umurtan Malamai su koma aiki ranar. Su kuma dalibai ana shawartarsu su yi biyayya don kansu."
Gwamnatin Tarayya Zata Bude Jami'o'i Duk Da Yajin Aikin ASUU
Alamu sun bayyana cewa gwamnatin tarayya na shirin bude jami'o'in Najeriya duk da yajin aikin kungiyar Malaman jami'a watau ASUU.
A cewar majiyoyi a ma'aikatar Ilimi, Malamai kadai ne ma'aikatan jami'an da suka rage basu komai aiki ba saboda tuni sauran ma'aikatan jami'a irinsu NASU, da SSANU sun janye daga yaji.
Wannan ya biyo bayan zaman da ma'aikatar Ilimi ta shirya da shugabannin jami'o'i ranar Talata mai zuwa.
Rahoton Vanguard a bayyana cewa za'ayi wannan zama ne a ofishin hukumar jami'o'in Najeriya NUC dake Abuja tare da Ministan Ilimi, Adamu Adamu.
Asali: Legit.ng