Hotuna: An Bude Katafaren Masallacin Kaltungo, jihar Gombe Ranar Juma’a

Hotuna: An Bude Katafaren Masallacin Kaltungo, jihar Gombe Ranar Juma’a

An bude sabon katafaren Masallacin Juma'a a garin Kaltungo dake karamar hukumar Kaltungo dake jihar Gombe.

An kaddamar da wannan babban Masallacin ne ranar Juma'a, 26 ga watan Agusta, 2022.

Daga cikin wadanda suka halarci taron bude Masallacin akwai Gwamnan jihar Gombe, Alhaji Muhammad Inuwa Yahaya; tsohon gwamnan jihar Bauchi na mulkin soja, Alhaji Rasheed Adisa Raji; Ministan Sadarwa, Farfesa Isa Ali Pantami.

Hakazalika akwai Mai Martaba Shehun Borno, Alhaji Abubakar bn Umar bn Amin Elkaneni, da A chikin mahalarta taron akwai, Mai martaba Sarkin Dutse, Mai martaba Mai Fika, Mai martaba Sarkin Dukku, Mai martaba Sarkin Deba, Mai martaba Sarkin Shani, Mai martaba Sarkin Gaya, Mai martaba Polo Dadiyo.

Ministan Sadarwa, Malam Pantami, ne ya gabatar da Lakca inda yayi magana akan muhimmancin Masallaci matsayin wajen neman ilimi da wayar da kan jama'.

Kara karanta wannan

Jerin Gwamnonin Najeriya 8 Da Suka Kwancewa Sarakuna Rawani a Jihohinsu

Kalli hotunan:

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Kaltungo
Hotuna: An bude katafaren Masallacin Kaltungo, jihar Gombe ranar Juma’a Hoto: Professor Isa Ali Pantami
Asali: Facebook

Kaltungo
Hotuna: An bude katafaren Masallacin Kaltungo, jihar Gombe ranar Juma’a Hoto: Professor Isa Ali Pantami
Asali: Facebook

KAltungo
Hotuna: An bude katafaren Masallacin Kaltungo, jihar Gombe ranar Juma’a
Asali: Facebook

Kaltungo
Hotuna: An bude katafaren Masallacin Kaltungo, jihar Gombe ranar Juma’a
Asali: Facebook

Asali: Legit.ng

Authors:
AbdulRahman Rashida avatar

AbdulRahman Rashida

Tags: