Jerin Gwamnonin Najeriya 8 Da Suka Kwancewa Sarakuna Rawani a Jihohinsu
- Kwancewa Sarakuna rawani wani abu ne da aka dade ana yi tun lokacin Sir Ahmadu Bello Sardauna
- Tun dawowar Demokradiyya Najeriya, gwamnoni sun cire Sarakuna a jihohin bisa dalilai da dama
- Sarakuna sama da goma aka kwance rawani tun da aka dawo da Demokradiyya a 1999
Kwancewa Sarkin gargajiya rawani a Najeriya abu ne wanda aka dade ana yi tun bayan samun yancin Najeriya daga hannun turawan mulkin mallaka.
Tun dawowar demokradiyya a 1999, sabani, rashin jituwa musamman na siyasa ya yi sanadin cire rawanin wasu Sarakuna a Arewa da Kudancin Najeriya.
Tare da TheNation, Mun tattaro muku jerin wasu gwamnoni a Najeriya da suka taba kwance rawani sarkin a zamaninsu
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Na baya-bayan nan shine Gwamna Kano, Abdullahi Umar Ganduje, wanda ya tsige Sarkin Kano, Muhammadu Sanusi na biyu.
Kundin tsarin mulkin Najeriya ya baiwa gwamnoni karfin tsige Sarki a Najeriya.
Ga jerin gwamnonin da suka cire Sarakuna:
1. Bello Matawalle, Zamfara, 2022
Gwamna Matawalle ya cire Sarkin Zurmi, Abubakar Atiku, Sarkin Dansadau, Hussaini Umar, da Sulaiman Ibrahim, Dagacin Birnin Tsaba bisa zargin hada kai da yan bindiga
2. Abdullahi Ganduje, Kano, 2020
Gwamna Kano, Abdullahi Umar Ganduje, ya tsige Sarkin Kano, Muhammadu Sanusi na biyu bisa zargin shiga harkar siyasa
3. Willie Obiano, Anambra 2020
Ya tsige Igwe Chijioke Nwankwo of Nawfia, Igwe Anthony Onyekwere of Owelle da Igwe G. B. C. Mbakwe of Abacha.
4. Nyeson Wike, Rivers, 2019
Ya tsige Sarkin Baabe
5. Olusegun Mimiko, Ondo, 2010
Ya tsige Deji of Akure of Akure Oba Oluwadamilare Adesina Osupa III bisa dukkan matarsa a cikin fada
6. Adams Oshiomhole, Edo, 2016
Ya tsige Anslem Aidenojie (Onojie of Uromi) bisa zagin wata mata kuma ya ki bada hakuri. Amma daga baya Gwamna Godwin Obaseki ya mayar da shi
7. Martin Elechi, Ebonyi, 2013
Ya tsige Eze Joseph Oko. Ivi of Akaeze bisa yawan shan giyansa yayinda ya tsoge Eze Micheal Orji bisa adawa da gwamnati.
8. Muhammad Adamu Aliero, Kebbi, 2005
Ya tsige Sarkin Gwandu Mustapha Jokolo bisa kalaman da basu dace ba
Asali: Legit.ng