Bayan Kwanaki 30 a Tsare, An Sako Shahrarren Lauya Daga Kurkuku

Bayan Kwanaki 30 a Tsare, An Sako Shahrarren Lauya Daga Kurkuku

  • Bayan kwanaki talatin a gidan gyara hali da Alkali ta jefashi, lauya a jihar Akwa Ibom ya samu yanci
  • Kungiyar Lauyoyin Najeriya NBA ta yi barazanar shigar da Alkalin kotu bisa wannan abu
  • Barista Inibehe Effiong ya kasance Lauyan jam'iyyar African Action Congress wata AAC na Omoyele Sowore

ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit

Akwa Ibom - An sako shahrarren Lauya, Barista Inibehe Effiong, daga gidan gyara hali bayan kwashe kwanaki 30 da aka yanke masa kan laifin raini ga Alkali.

Babbar Alkalin jihar Akwa Ibom, Ekaette Obot, ta jefa Effiong gidan yari ne bayan gardama da yayi da ita yayin wani zaman kotu.

Lauyan ya samu yanci ne misalin karfe 8 na safe yayinda masoyansa suka cika wajen kurkukun don tarbansa, rahoton tvcnews.

Yace:

"Karramawa ne gareni a daure ni kan gaskiya. Muryata ba zata dusashe ba har abada."

Kara karanta wannan

Da Duminsa: Bene Mai Hawa Biyu ya Ruguje, Ya Danne Ma'aikata Masu Tarin yawa a Abuja

Inibehe
Bayan Kwanaki 30 a Tsare, An Sako Shahrarren Lauya Daga Kurkuku Hoto: @tvcnewsng
Asali: Twitter

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Kotun Saudi Ta Yankewa Tsohon Limamin Ka’aba Daurin Shekara 10 a gidan yari

A wani labarin kuwa, a ranar Litinin, 23 ga watan Agusta 2022, wata kotu da aka kafa domin sauraron laifuffuka na musamman ta yanke hukunci ga Saleh al Talib.

Middle East Eye ta fitar da labari cewa an Sheikh Saleh al Talib da laifi, kuma an yanke masa hukuncin daurin shekaru 10 a gidan yari a Saudi Arabiya.

Kotun daukaka karar tayi fatali da hukuncin da aka yi a baya, inda aka wanke Sheikh Al Talib wanda tsohon limami ne a masallacin Harami a Makkah.

Asali: Legit.ng

Authors:
AbdulRahman Rashida avatar

AbdulRahman Rashida