Ma'aikatan Hukumar Jin Dadin Yan Sanda Sun Tafi Yajin Aikin Sai Baba Ta Gani

Ma'aikatan Hukumar Jin Dadin Yan Sanda Sun Tafi Yajin Aikin Sai Baba Ta Gani

  • Ma'aikatan Hukumar Jin Dadin Yan Sanda Watau Police Service Commission Sun Tafi Yajin Aiki
  • Suna zargin Sifeton yan sanda IGP da yiwa dokokin hukumar katsalandan tare da watsi da hukuncin kotun daukaka kara
  • Hukumar PSC ta kwan biyu tana sa'insa da Hukumar Yan sanda tun lokacin tsohon IGP Mohammed Adamu

ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit

Abuja - Gamayyar ma'aikatan hukumar kula da yan sanda PSC ta sanar da tafiya yajin aiki ga shugabanta bisa saba alkawuran da akayiwa ma'aikatan.

Gamayyar ta bayyana cewa zasu fara yajin aikin ne ranar Litinin, 29 ga watan Agusta, 2022.

Shugaban gammayar, Mr Adoyi Adoyi, ya bayyana haka a hira da manema labarai ranar Alhamis a Abuja, rahoton Punch.

Ya ce sun yanke shawarar tafiya yajin ne sakamakon rashin jituwa dake gudana tsakanin shugaba hukumar, Musuliu Smith da Sifeto Janar na yan sanda, Usman Baba, lamarin daukan sabbin yan sanda, karin girma, dss.

Kara karanta wannan

Tashin hankali: Rikicin addini ya barke tsakanin kirista da 'yan gargajiya, an kashe wani

PSC/IGP
Ma'aikatan Hukumar Jin Dadin Yan Sanda Sun Tafi Yajin Aikin Sai Baba Ta Gani
Asali: Facebook

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Yace kara da cewa Sifeton yan sanda IGP gaba daya yana yiwa dokokin hukumar katsalandan tare da watsi da hukuncin kotun daukaka kara.

A cewarsa:

"Zamu tafi yajin aiki ne daga ranar Litnin, 29 ga Agusta, don nuna rashin amincewarmu da yadda Shugaban hukumarmu ke jagoranci da kuma sabawa umurnin kotu da Sifeto Janar IGP Usman Baba, ke yi."
"Aikin hukumar PSC a bayyane yake amma a kundin tsarin mulki amma IGP duk ya yi watsi da su, ya kwace ayyukan hukumar. Shi ke nadin mutane kuma yake garin girma sabanin abinda doka ta tanada."
"A bisa kundin tsarin mulki, nadin mukamai, karin girma, da daukan sabbin yan sanda duk aikin PSC ne ba IGP ba."

Yan Sanda Sama da 1,000 Sun Yi Zanga-Zangan Kan Rashin Biyansu Albashi a Kwara

Kara karanta wannan

Diraktan Hukumar FCCPC Ya Mutu Bayan Fada Da Abokiyar Aiki a Katsina

A wani labarin kuwa, aƙallla jami'an hukumar yan sanda 1,056 ne suka fito zanga-zanga kan rashin biyan su Albashi na tsawon watanni 16 da gwamnatin jihar Kwara ta rike musu.

The Nation ta ruwaito cewa Yan sandan sun mamaye muhimman wurare yayin zang-zangar, wanda suka haɗa da Challenge, Post Office da Titin Ahmadu Bello wanda ke zuwa har gidan gwamnati.

Yayin zanga-zangar kuratan yan sandan, sun rinka rera, "Gwamnatin jihar Kwara, a biya mu Albashin mu na watanni 16."

Asali: Legit.ng

Authors:
AbdulRahman Rashida avatar

AbdulRahman Rashida