Mara Lafiya Ya Tashi Daga Gadon Asibiti, Ya Bi Budurwa Da Gudu Bayan Ta Dauki Wayarsa

Mara Lafiya Ya Tashi Daga Gadon Asibiti, Ya Bi Budurwa Da Gudu Bayan Ta Dauki Wayarsa

  • Wani bidiyon dake tashe a kafafen sada zumunta ya nuna wani mara lafiya ya kurewa wata mata gudu a asibiti
  • Abinda ya baiwa mutane mamaki shine mutumin mara lafiya ne dake kwance a gadon asiitin amma ya tashi ya fita da gudu
  • Daga baya aka gano ta dauki wayarsa ne tana dubawa kuma ana kyautata zaton budurwarsa ce

ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit

Wani abin dariya ya faru a asibiti yayinda wani mutumi ya fito daga gadon asibiti kuma ya kurewa wata budurwa gudu don ya kwato wayarsa da ta dauka tana dubawa.

Budurwar da ake kyautata zaton masoyiyarsa ce tana kokarin guduwa daga asibitin tana duba wayar.

Mara LAfiya
Mara Lafiya Tashi Ya Daga Gadon Asibiti, Ya Bi Budurwa Da Gudu Bayan Ta Dauki Wayarsa Hoto: @danieljean56
Asali: Instagram

Ya kure mata gudu

Abinda ya ja hankalin mutane ne lokacin da ya fito daga kan gado ya bi ta da gudu.

Kara karanta wannan

Hikima: Fasihi ya kirkiri bandakin da mutane za su totsa toroso, sannan a biya su kudi

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

A bidiyon da @denieljean56 ya daura, mara lafiya na kokarin kamata kuma wata malamar jinya na kallon ikon Allah.

Malamar jinyar na binsa ta maida shi asibiti amma bai daina gudu ba yana kokarin kwace wayarsa hannun matar mai suna Lisa.

Kalli bidiyon:

Mabiyanmu sun bayyana ra'ayoyinsu:

Aminu Salisu Barkum yace:

"Abinda yakoro bera daga rami har yafada wuta tofa yafi wutar zafi."

Bin Siyuɗi yace:

"Akwai abun da ya gani wallahi"

Abdulganiyu Usman Bafeto:

"Normal ne ai saboda shikadai yasan meye acikin wayar nashi."

Amb Ahmad Bala Imam

"Yanada gaskia ai baa wasa da Nunawa uwar miji yatsa"

Abdo Daura yace:

"Ai a zamanin nan ko kwanciya zakai ka kwanta da addar yadda ko mafarki kai wani ya satar maka waya sai ka fille masa kai."

Kara karanta wannan

Ya Rabu Dani Saboda Ina Da Muni: Hotunan Sauyawar Wata Budurwa Shekaru Bayan Saurayi Ya Guje Ta Ya Ba Da Mamaki

Ya Rabu Da Ni Saboda Na Shiga Aikin Soja, Jarumar Soja Tayi Magana da Tsohon Saurayinta

Wata Sojar Najeriya ta bayyana yadda wani saurayinta ya nuna mata kiyayya kawai don ta shiga aikin Soja.

Budurwar ta bayyana hakan ne yayinda ta saki hotunanta a manhajar TikTok sanye da kayan Soja.

A hoton farko, ta sanya hoton Soja tana tsugunne.

Sannan a wani hoto ta nuna yanzu tayi zurfi cikin harkar Soja, ta shiga 'Special Force'.

Asali: Legit.ng

Authors:
AbdulRahman Rashida avatar

AbdulRahman Rashida