Maganar Tsige Buhari: Fadar Shugaban Kasa ta Caccaki Yan Jarida
- Yayinda wa'adin makonni shida da majalisa ta yiwa Shugaban kasa ke gabatowa, mai magana da yawunsa ya sake kareshi
- Malam Garba Shehu ya caccaki wata jarida dake kira ga a gaggauta tsige Shugaba Muhammadu Buhari
- Yan majalisar APC da PDP sun tafi hutun makonni shida inda sukayi barazanar tsige shugaban kasa
ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit
Abuja - Fadar Shugaban kasa ta yi watsi da maganar tsige Shugaba Muhammadu Buhari inda tace an tsige shugaban kasa ne kawai idan ya aikata wani babban laifi kuma aka tabbatar.
Yan malisar dokokin tarayya a makonnin baya sun yi barazanar tsige Shugaba Buhari kan gazawarsa wajen magance matsalar tsaro.
Yan majalisar dattawa da na wakilai sun yi ittifaki wajen baiwa shugaban kasan makonni shida ya magance matsalar tsaro ko su tsige shi.
Leadership ta ruwaito mai magana da yawun shugaban kasa, Malam Garba Shehu, ya yi martani da jawabin da kamfanin jaridar The Guardian, ya wallafa ranar Litnin, 22 ga Agusta, 2022 mai take: "A tsige Buhari kan rashin iyawarsa".
DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka
Malam Garba Shehu yace tuni wannan jaridar bata son Shugaba Buhari ko kadan tun da ya hau mulki, riwayar TheNation.
Shehu yace ana tsige shugaban kasa ne kawai idan ya aikata laifi kuma akwai hanyar da ake bi wajen yi.
A cewarsa:
"Jaridar Guardian, wacce ta zama yar adawar shugaban kasa da jam'iyyarsa APC tsawon shekaru yanzu ta wuce gona da iri wajen kira ga a tsige shugaban kasa."
"Editocin jaridar ba su son yadda shugaban kasan ke mulkin kasar saboda haka kawai a tsigeshi.
"Da alamun tsige shugaban kasa ya zama sabon abun da yan adawa ke amfani da shi wajen nuna kiyayyarsu gareshi (Buhari)."
"Saboda tun daga ranar da ya hau mulki suka fara zaginsa fiye da kowani shugaba a tarihin Najeriya. Sun gaza kayar da shi a zabe a 2019 kuma sun ga alamu yanzu APC zata lashe zaben 2023, saboda haka sun fara neman hanyoyin ganin karshensa."
"Bai zama dole jaridar Guardian ta zama abokiyar Shugaba Buhari ba, amma su daina irin wadannan labarai."
Asali: Legit.ng