Kwanan Nan Zamu Bayyana Sunayen Manyan Mutanen Dake Satar Mai, Fadar Shugaban Kasa

Kwanan Nan Zamu Bayyana Sunayen Manyan Mutanen Dake Satar Mai, Fadar Shugaban Kasa

  • Fadar Shugaban kasa ta yi barazanar bayyana sunayen Attajiran dake satar arzikin man Najeriya
  • Fadar ta ce abin takaicin shine yanzu har da jami'an tsaro ake hada baki wajen sace arzikin man feturin Najeriya
  • Kulli yaumin ana wawurar dukiyar Najeriya sakamakon fasa bututun mai ana kwashe danyan mai

Abuja - Mai magana da yawun shugaban kasa, Malam Garba Shehu ya bayyana cewa kwanan da za'a bayyana sunayen manyan mutanen da ke daukar nauyin satar danyan mai a Najeriya.

Garba Shehu ya bayyana hakan ne ranar Juma'a yayin shirin 'Daily Politics' na tashar Trsut TV.

Ya ce yanzu har da jami'an tsaro ake hada baki wajen sace arzikin man feturin Najeriya.

Garba Shehu
Kwanan Nan Zamu Bayyana Sunayen Manyan Mutanen Dake Satar Mai, Fadar Shugaban Kasa Hoto: Garba Shehu
Asali: Facebook

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Kara karanta wannan

Zamu Dira Kan Barayin Man Fetur A Neja-Delta, Shugaba Buhari

A cewarsa:

"A baya muna rokon OPEC ta bari mu rika fitar da mai da yawa, yanzu ta bamu izini amma mun gaza. Wannan abin kunya ne."
"Ina kyautata zaton cewa nan da yan kwanaki mai da shawaran tsaro na kasa (NSA) zai bayyanawa yan Najeriya manyan mutanen da ke aikata wannan laifi na sata saboda ana kamasu kuma ana kona matatun man su."
"Kamfanin NNPC kuwa tana 'dana na'urorin sanya ido don gani duk lokacin da aka yi kokarin fasa bututun mai."
Wasu lokutan har da hannun jami'in tsaro. Abu ya yi muni"

Zamu Dira Kan Barayin Man Fetur A Neja-Delta, Shugaba Buhari

Shugaba Muhammadu Buhari ya bayyana cewa za a karfafa tsaro domin dakile masu satar danyan man Najeriya.

Buhari ya bayyana hakan ne mako guda bayan da aka damke jirgin ruwa yana kokarin satar man Najeriya.

A ranar 12 ga Agusta, Jami'an Sojin ruwan Najeriya sun damke wani jirgin ruwa, (MT) HEROIC IDUN, mallakin kamfanin Hunter Tankers AS dake Scandinavia, Norway yana kokarin satar danyan mai a Najeriya.

Kara karanta wannan

Harin Jirgin kasa: 'Dan Uwan Budurwar da Shugaban Yan Bindiga Ke Kokarin Aurawa Kansa Ya Koka

Hukumar ta bayyana cewa jirgin ruwan ya isa rijiyar man ne cikin daren 7 ga Agusta da niyyar satar mai amma jami'anta suka dakilesu.

Saidu Garba ya cigaba da cewa sakamakon haka suka umurci direban jirgin ya jira sai NNPC ya bashi izini, amma Direban ya kurewa jirginsa gudu kuma ya nufi kasar Sao Tome and Principe, riwayar TheCable.

A cewarsa, daga baya aka damke jirgin ruwan a kasar Equatorial Guinea bayan kure masa gudu.

Babban Lauyan kasar Equitorial Guinea, Anatalio Nzang Nguema, ya bayyanawa tashar Talabijin na TVGE cewa an damke mutum 25 ke cikin jirgin.

Sun hada da yan kasar Indiya 16, yan kasar Sri Lanka 7, dan kasar Poland daya da kuma dan kasar Filibbin daya.

Asali: Legit.ng

Authors:
AbdulRahman Rashida avatar

AbdulRahman Rashida