Da dumi-dumi: Masu Garkuwa Sun Yi Awon Gaba da Amarya da Ango a Katsina
- Yan bindiga sun kuma kai wani sabon hari cikin garin Katsina Arewa maso yammacin Najeriya
- Katsina na cikin jihohin yankin Arewa maso yammacin Najeriya da ke fuskantar matsin rikicin yan bindiga masu garkuwa
- Kakakin hukumar ‘yan sandan jihar Katsina ya ce jami’ansu sun dukufa don kuɓutar da amarya da angon
ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit
Katsina - Wasu da ake zargin ya bindiga ne masu garkuwa da mutane sun yi awon gaba da Amarya da Ango biyo bayan harin da suka kai unguwar Shola dake jihar Katsina.
A bisa rahoton BBC, mazauna unguwar sun bayyana yadda 'yan bindigar suka far musu cikin dare kuma suka kwashe sa'a daya suna artabu da jami'an sa kai.
Sun bayyana cewa yan bindigan sun hallaka wasu 'yan sa kai biyu da ke kokarin kare mutane.
Wani mazaunin unguwar ya shaida wa sashen Hausa na BBC cewa ‘yan bindigan sun shiga unguwar ne bisa babura dauke da bindigogi suna harbe-harbe.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Kawo yanzu dai an tabbatar da rashin rayuka biyu da kuma garkuwa da dimbin mutane cikin har da sabbin ma'aurata biyu.
Kakakin rundunar ‘yan sandan jihar Katsina SP Gambo Isah ya tabbatar da aukuwar wannan hari, inda ya ce jami’ansu sun dukufa don kuɓutar da amarya da angon.
Asali: Legit.ng