Matsin Rayuwa: Farashin Litar Kalanzir ya kai N800, Ƴan Najeriya sun Shiga Halin Ha'u'la'i
- Farashin kalanzir din girki a Najeriya yayi tashin gwauron zabi inda ake siyar da shi kan N800 zuwa N850, har N1000 a sassan kasar
- Hukumar kididdiga ta NBS tace farashin kalanzir da iskar gas sun tashi da kashi 88 a cikin shekara daya tak a fadin Najeriya
- Masana sun alakanta hakan da yadda Najeriya bata iya tace danyen man fetur dinta da kanta da kuma tashin dala tare da faduwar darajar Naira
ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit
Farashin kalanzir wanda iyalai da yawa ke amfani da shi, yayi tashin gwauron zabi zuwa N800 matsayin kudin lita daya saboda yadda kasuwar ke kokarin juyawa tare da daidaitawa zuwa sabon karin farashin man fetur da iskar gas.
Binciken kasuwa da The Punch tayi a ranar Talata ya bayyana cewa, a makon da ya gabata an siyar da kalanzir kan farashin N700 lita daya amma yanzu ana siyar da shi kan N800 zuwa N850 a wasu sassan birnin Legas, yayin da farashin ya kai N1000 a wasu wuraren.
Tsohon Shugaban Kasar Najeriya Ya Koka Kan Tsadar Rayuwa, A Yayin Da Farashin Kayayyaki Ke Cigaba Tashi A Kasar
A Ghana, farashin litar kalanzir a halin yanzu ya kai N585 wanda daidai yake da GH 12.044.
Ba kamar fetur ba, farashin kalanzir yana kafuwa ne daga 'yan kasuwa ba kamar wanda gwamnati ke kayyadewa ba.
DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar
"'Yan kasuwa ke tsayar da farashinsa. Dala ce da farashin danyen man fetur a kasuwar duniya ke samar da farashin kalanzir. Tunda ya kasance hakan, farashin kan yi sama kuma ya sauko kasa," Shugaban bangaren ayyuka na 'yan kasuwar kayayyakin man fetur masu zaman kansu na Najeriya, IPMAN, Mike Osatuyi ya sanar.
A watan Yunin da ya gabata, Hukumar kididdiga ta NBS, ta rahoto cewa an samu tashin farashin kalanzir da iskar gas da kashi 88 a cikin shekara daya.
Kamar yadda rahoton NBS ya nuna, farashin kalanzir ya tashi da kashi 86.94 a cikin shekara daya.
Rahoton ya bayyana cewa, masu amfani da kalanzir a gidaje a watan Mayun 2022 sun samu karin farashinsa da kashi 15.21 a wata daya bayan daya, daga N589.82 a watan Afirilun 2022 zuwa N679.54 a watan Mayun 2022.
Farashi a jihohi kuwa ya nuna cewa, an siya kalanzir mafi tsada a jihar Enugu kan N868.75 a watan Mayun 2022, Ebonyi ke biye da N861.11 sai Imo N801.97. A daya bangaren, an siya kalanzir mafi arha a jihar Bayelsa kan farashi N558.06, sai Yobe kan N601.39 da Nasarawa kan N603.33.
Wani kwararre a harkar makamashi mai suna Bala Zakka, ya alakanta wannan tashin gwauron zabin da yadda Najeriya bata iya tace man fetur domin masu amfanin cikin gida.
Sakataren IPMAN, Olufemi Adewole, ya sanar da Punch cewa dalilin wannan cigaba da rashin farashin kalanzir din shi ne yadda dala ke ta hawa yayin da naira ke kara lalacewa.
Asali: Legit.ng