Matashi Dan Shekara 27 Ya Koka Da Rashin Samun Aiki Saboda Ana Yi Masa Kallon Karamin Yaro

Matashi Dan Shekara 27 Ya Koka Da Rashin Samun Aiki Saboda Ana Yi Masa Kallon Karamin Yaro

  • Wani mutumin kasar China mai shekaru 27, Mao Sheng ya ce yana fuskantar matsaloli wajen samun aiki
  • A cewar matashin, baya samun aiki saboda yanayin halittarsa da ke sa shi kama da karamin yaro
  • Mao ya ce kamfanoni da dama sun ki daukarsa aiki saboda a cewarsu basa so a kama su da laifin bautar da karamin yaro

ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit

Wani dan kasar China, Mao Sheng, mai shekaru 27 ya bayyana matsalolin da yake fuskanta saboda kankantar halittarsa.

Mutumin wanda aka haifa kuma ya tashi a China, Mao Sheng ya kasance baida aikin yi saboda kankantar jikinsa.

Mao ya ce kamfanoni na kin karbarsa saboda basa so a alakanta su da bautar da karamin yaro saboda yanayinsa.

Dan China
Matashi Dan Shekara 27 Ya Koka Da Rashin Samun Aiki Saboda Ana Yi Masa Kallon Karamin Yaro Hoto: Yahoo news /The Sun
Asali: UGC

A cewar Mao, wasu kamfanonin sun nace cewa an turo masu shi ne a matsayin mai leken asiri don fallasa kamfanonin da ke daukar kananan yara aiki.

Kara karanta wannan

Ke duniya: A kan N50,000, matashi ya halaka kawar kanwarsa, ya birne gawarta a dakinsa

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Yahoo News ta rahoto cewa matashin wanda zuciyarsa ta karye ya nuna katin shaidarsa kwanaki biyu bayan nan don tabbatar da cewar an haife shi a 1995 ga wadanda ke da shakku kan labarinsa.

Mao ya koka da halin da mahaifinsa ke ciki

Mao ya ci gaba da bayyana yadda shi da abokinsa suka nemi aiki a kamfani daya, amma manajan ya dauki abokinsa kadai, sannan ya share shi.

Mutumin da ke cike da bakin ciki da halin da yake ciki ya bayyana cewa shi kadai ne me zai iya taimakawa mahaifinsa da ke fama da shanyewar barin jiki.

Da yake bayar da labarinsa, matashin ya koka yayin da yake kokarin tabbatarwa mutane cewa shi ba yaro bane kamar yadda jikinsa ke nunawa. Ya ce a shirye yake yayi duk aikin da zai samu kudi mai kyau don kula da mahaifinsa.

Kara karanta wannan

Tana Tara Kudi: Bidiyon Yadda Wata Mata Ta Koma Rayuwa Cikin Motarta Saboda Ba Za Ta Iya Biyan Kudin Haya Ba

Bidiyon Yadda Wata Mata Ta Koma Rayuwa Cikin Motarta Saboda Ba Za Ta Iya Biyan Kudin Haya Ba

A wani labarin, Nikita Crump, wata yar Arewacin Carolina mai mabiya sama da miliyan 1 a TikTok ta ba da labarin yadda take gudanar da rayuwarta a cikin mota.

A bisa ga rahoton New York Post, matar ta yanke shawarar komawa cikin motarta kirar Honda Civic da zama bayan gwagwarmayar da take sha na biyan kudin haya kan lokaci da tsallake cin abinci don tara kudi.

Hakan na faruwa duk da tarin basussukan da ke kanta yayin da take ayyuka guda biyu.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng