Za a fuskanci ambaliyar ruwa a watannin Augusta da Satumba a Najeriya, NiMet
- Hukumar kula da yanayi ta NiMet ta sanar da cewa za a fuskanci ambaliyar ruwa a watannin Augusta da Satumba
- Kamar yadda shugaban hukumar, Farfesa Mansur Bako Matazu ya sanar, wannan ya shafi sauyin yanayi a duniya
- Ya shawarci jama'a da ke kusa da wuraren da aka saba ambaliyar da su hanzarta tattara komatsansu su bar wurin
ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit
Najeriya zata fuskanci gagarumar ambaliyar ruwa a watannin Augusta da Satumba, kamar yadda hukumar kula da yanayi, NiMet ta tabbatar.
Shugaban NiMet, Farfesa Mansur Bako Matazu, ya bayyana hakan a wani shirin gidan talabijin na Channels TV a ranar Litinin.
Yace cibiyar ta bada shawarwari daban-daban akan ambaliyar ruwa wanda 'yan Najeriya suka ki kiyayewa.
Farfesa Matazu yace: "Za a samu karin yawan ruwan sama a watanni biyu masu zuwa. Zai fi yawa a watannin Yuli, Augusta da Satumba. Za mu fuskanci karin ambaliyar ruwa."
Hotuna da bidiyo: Dankareriyar daham din da Fatima Shettima ta saka wurin wushe-wushe ya dauka hankali
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
"Wannan abu ne da duniya baki daya ya kamata ta damu da shi saboda yana da alaka da sauyin yanayi kuma akwai abubuwan dake kawo shi.
"Don haka, za a samu karfin ambaliyar ruwa kuma muna shawartar MDAs ballantana a matakin jihohi da kananan hukumomi da su shawarci mutanen da ke kusa da wuraren da ake samun ambaliya ko za a iya samu da su tattara su bar wuraren," yace.
Asali: Legit.ng