Sanatocin Jam'iyyun Hamayya Sun Fice Daga Majalisa Bayan Kira a Tsige Buhari
- Wata hatsaniya ta ɓalle a zauren majalisar dattawan Najeriya bayan fatali da bukatar tattauna wa kan tsige shugaba Buhari
- Shugaban marasa rinjaye, Sanata Aduda, ya bukaci majalisar ta tattauna kan matsalar tsaro da kuma tsige Buhari
- Sanata Ahmad Lawan ya yi fatali da bukatar nan take, lamarin da ya fusata Sanatoci suka fice daga zauren
ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit
Abuja - Sanatocin jam'iyyun hamayya sun fice daga zauren majalisar Dattawa biyo bayan kira a tsige shugaban ƙasa, Muhammadu Buhari daga kujerarsa.
Channels TV ta ruwaito cewa hakan ya biyo bayan wata Dirama da ta auku a zaman mambobin majalisar Dattaawa ta ƙasa yau Laraba a Abuja, babban birnin ƙasa.
Shugaban marasa rinjaye, Sanata Phillip Aduda, ya tada mahawara inda ya nemi shugaban majalisa, Sanata Ahmad Lawan, a tattauna kan yanayin tsaron ƙasar nan da kuma tsige shugaba Buhari.
Amma Sanata Lawan, wanda ke jagorantar zaman, ya yi fatali da buƙatar shugaban marasa rinjaye, inda ya bayyana cewa batun da ya ɗakko ya faɗi warwas a kan fuska.
Domin nuna fushi da abinda shugaban majalisa ya yi, Sanatocin jam'iyyun adawa da ba APC ba, suka miƙe tsaye, suka fice daga majalisar ana tsaka da zaman yau.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Mun ba Buhari wa'adin mako shida - Aduda
Bayan abubuwan da suka faru, Sanata Aduda, ya yi jawabi ga manema labarai a bakin zauren majalisar a madadin fusatattun takwarorinsa.
A cewarsa, mambobin majalisar da ke ɓangaren adawa sun bai wa shugaban ƙasa, Muhammadu Buhari, mako Shida ya shawo kan matsalar tsaron da ta addabi Najeriya.
Bugu da ƙari, ya ce Sanatocin sun cimma matsayar cewa zasu fara bin matakan tsige shugaban ƙasa idan har ya gaza dawo da zaman lafiya a Najeriya cikin lokacin da suka ɗibar masa.
A wani labarin kuma Gwamnoni arewa uku da wasu jiga-jigan APC sun sa labule da Tinubu, Shettima a Abuja
Gwamna El-Rufai na jihar Kaduna da wasu gwamnonin arewa biyu sun ziyarci jagoran APC na ƙasa, Bola Ahmed Tinubu a Abuja.
Abokin takarar Tinubu, Sanata Kashin Shettima, Sakataren APC na ƙasa da tsohon shugaba, Oshiomhole sun halarci taron.
Asali: Legit.ng