Ka gaji ka koma Daura: Femi Falana ya Fadawa Shugaba Buhari

Ka gaji ka koma Daura: Femi Falana ya Fadawa Shugaba Buhari

  • Lauyan kare hakkin dan Adam Femi Falana ya shawarci shugaban kasa Muhammadu Buhari da ya sauka daga mulki saboda ya gaji
  • Femi Falana ya ce al'umuran yan Najeriya ya kara tabarbarewa a karkashin gwamnatin shugaba Buhari
  • Falana yace duk da Buhari ya shaidawa yan Najeriya cewa ya gaji bai hana shi yawuce-yawuce kasashen Duniya ba

Jihar Legas - Lauyan kare hakkin dan Adam Femi Falana ya shawarci shugaban kasa Muhammadu Buhari da ya sauka haka, saboda ya gaji.

Babban Lauyan Najeriya, wanda ya yi jawabi a zanga-zangar da kungiyar kwadago ta Najeriya NLC ta gudanar a Legas, ya koka kan yadda lamuran ‘yan Najeriya ke kara tabarbarewar wanda ya shafi fannin tattalin arziki zuwa yajin aikin ASUU.

Ya ce:

BUHARI
Ka gaji ka koma Daura: Femi Falana ya Fadawa Shugaba Buhari FOTO THE NATION
Asali: UGC
“Mun hallara a wannan filin zanga-zangar ne a yau, domin nuna kin amincewar mu da yaudarar gwamnatin Buhari.

Kara karanta wannan

Muhimmacin Ziyarar Shugaba Buhari Kasar Liberia - Garba Shehu

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

“Kamar yadda rayuwar ‘yan Najeriya ke kara tabarbarewa kowace rana. Ba mu zabi wannan gwamnatin dan ta jawo wa ’yan Najeriya wahala ba. Yanzu wahala, ta’addanci, koma bayan tattalin arziki sun mamaye kasarmu.
“Buhari yana yawuce-yawucen kasashen duniya, amma ya shaida mana cewa ya gaji. Don haka dole ne Buhari ya sauka. Dole ne ya sauka.
"Ina goyon bayan malamai masu yajin aiki, da kuma ƙungiyar ASUU."

Muhimmancin Ziyarar Shugaba Buhari Kasar Liberia - Garba Shehu

A wani labari kuma, Abuja - Fadar shugaban kasa a ranar Litnin ta sanar da cewa Shugaba Buhari zai tafi kasar Laberiya halartan bikin murnar ranar yancin kasar ta 175.

Buhari zai tafi Laberiya ne biyo bayan barazanar yan bindiga masu garkuwa da mutane inda suka fara kai hare-hare cikin birnin tarayya Abuja.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Tofa avatar

Ibrahim Tofa