'Yan Bindiga Sun Buɗe Wa Matafiya Wuta, Sun Kashe Wasu Sun Sace Da Yawa a Katsina

'Yan Bindiga Sun Buɗe Wa Matafiya Wuta, Sun Kashe Wasu Sun Sace Da Yawa a Katsina

  • Tsagerun yan bindiga sun kai hari kan matafiya a kan hanyar Katsina zuwa Jibiya, sun kashe aƙalla mutum uku
  • Wani shaidan da abun ya faru a kan idonsa ya ce maharan sun toshe hanyar, suka kwashi mutanen motoci huɗu
  • Wannan na zuwa ne yayin da yan Najeriya ke ta Allah wadai da azabtarwan da yan ta'adda ke yi wa fasinjojin jirgin ƙasa

Katsina - A ranar Lahadin nan, 'Yan ta'adda sun farmaki matafiya a kan hanyar Katsina-Jibiya a jihar Ƙatsina, sun halaka mutuum uku kuma sun yi awon gaba da wasu da dama.

Wata majiya mai karfi, wanda harin ya faru a gabansa, ya shaida wa jaridar Leadership cewa ya ga mutane da dama ɗauke da raunin harbi lokacin da maharan suka buɗe musu wuta.

Miyagun yan bindiga sun kai hari jihar Katsina.
'Yan Bindiga Sun Buɗe Wa Matafiya Wuta, Sun Kashe Wasu Sun Sace Da Yawa a Katsina Hoto: leadership
Asali: UGC

Ya ce maharan sun buɗe wa wata motar haya ta Katsina State Transport Authority (KSTA) wuta tare da wasu motoci da ke ɗauke da mutane a kan hanyar.

Kara karanta wannan

Tashin hankali: 'Yan bindiga sun tari motar gwamnati, sun sheke direba, sun sace fasinjoji sama da 30

A cewar mutumin, Direban Motar Bas ɗin mallakin gwamnatin jiha mai lambar rijista KT 14D-58 KT na faya daga cikin mutum uku da suka rasa rayuwarsu a harin.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Shaidan ya ƙara da cewa yan bindigan sun kuma shiga ƙauyen Farun Bala, inda suka tattara dabbobi da sauran kayayyaki mallakin mazauna ƙauyen suka yi gaba da su, kamar yadda Channels ta ruwaito.

Mutumin ya ce:

"Yan bindigan sun tare hanyar Katsina zuwa Jibiya lokacin da suka kawo farmaki bisa tilas motoci suka tsaya kuma lamarin ya faru ranar kasuwar mako ta Jibiya, ranar da motoci ke amfani da hanyar sosai."
"Maharan sun tattara mutane da yawa na cikin motoci hudu, suka tilasta musu tafiya zuwa cikin jeji."

Majiyar, wacce ta bayyana cewa hanyar Katsina-Jibiya na da aƙalla shingen bincike 20 na jami'an tsaro haɗi da na kwastam, ya nuna takaicin yadda ba su yi komai na hana ta'addancin ba.

Kara karanta wannan

Yanzu-Yanzu: Hoton Osinbajo Na Farko Bayan Masa Tiyata Ya Bayyana

Wane mataki hukumomi suka ɗauka?

Shugaban ƙaramar hukumar Jibiya, Bishir Maitan, ya tabbatar da faruwar lamarin, Sia dai har yanzun hukumar yan sandan Katsina ba ta ce uffan ba.

A wani labarin kuma 'Yan ta'addan da ke tsare da fasinjojin jirgin ƙasan Kaduna zuwa Abuja sun saki sabon bidiyo

Bidiyon ya nuna yadda suke azabtar da mutanen da ke hannun su da duka, kuma sun yi barazanar kai Najeriya ƙasa.

Ɗaya daga cikin fasinjojin jirgin wanda ya yi magana a Bidiyon ya roki kasashen duniya su saka baki.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262

Tags: