Sallar Nafila Lokacin Da Liman Ya Hau Minbari Ranar Jumu'ah, Sheikh Jabir Sani Maihula

Sallar Nafila Lokacin Da Liman Ya Hau Minbari Ranar Jumu'ah, Sheikh Jabir Sani Maihula

Sheikh Dr Jabir Sani Maihula, shine shugaban tsangayar nazarin addinin Musulunci ta jami'ar jihar Sokoto kuma babban malamin addinin mazauni cibiyar daular Islamiyya.

A wannan sako, ya yi bayani kan yin Sallar Nafila yayinda Liman ya hau minbari gabatar da hudubar juma'a.

1) Idan mutum ya shiga masallaci ranar Jumu'ah liman yana akan minbari, zaiyi sallah raka'ah biyu, amma ya gajarta. (Bukhari da Muslim)

2) Idan mutum ya taradda ana kiran sallah kafin a fara khutbah, zaiyi sallah lokacin da ake kira bazai jira a gama kiran sallah ba, saboda sauraron khutbah wajibi ne amma sauraron maikiran sallah Sunna ne. ( Ibn Uthaimeen)

3) Idan mutum bai samu shiga masallaci ba ya tsaya a harabar masallaci, bazaiyi sallah ba lokacin da liman ke khutbah, saboda sallar ta Tahiyyatul masjid ce, bata wajaba sai ga wanda ya shiga masallaci.

Kara karanta wannan

Da dumi-dumi: Gwamnatin Buhari na duba yuwuwar haramta Okada a Najeriya

4) Mutane da yawa sukanyi kuskure sai su zata akwai wasu raka'ah biyu da akeyi kafin Jumu'ah, sai kaga mutum yazo yana wajen masallaci ya kabbarta sallah alhali liman yana khutbah. Wannan kuskure ne, matsayin sa kamar wanda ya tashi a cikin masallaci ya kabbarta sallah alhalin liman yana khutbah.

5) Duk wanda ya shiga masallaci wajibi ne (a kan zance mafi inganci) yayi sallah raka'ah biyu kafin ya zauna. Wannan hukuncin da ranar Jumu'ah da Assabar da sau ran ranaku duka daya ne. Dalili akan hakan shine, cewar da Manzon Allah S.A.W. yayi: Idan dayanku ya shiga masallaci kada ya zauna sai yayi sallah raka'a biyu. ( Bukhari da Muslim)

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ya kamata ayi fadakarwa da mutane akan wannan hukuncin, saboda da yawa akan saɓa."

Sheikh Jabir Sani Maihula

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng