Da Ɗumi-Ɗumi: Gwamna Matawalle ya haramta wa sarakunan Zamfara naɗin Sarauta

Da Ɗumi-Ɗumi: Gwamna Matawalle ya haramta wa sarakunan Zamfara naɗin Sarauta

  • Gwamnan jihar Zamfara, Bello Matawalle, ya haramta wa Sarakunan jihar naɗa kowane mutum sarauta har sai sun samu izini
  • A makon da ya gabata ne Najeriya ta ɗau zafi bayan masarautar Yandoto a Zamfara ta naɗa kasurgumin ɗan bindiga Sarauta
  • Tuni gwamnatin Zamfara ta soke nafin sarautar kuma ta ɗauki mataki domin kare faruwar irin haka nan gaba

Zamfara - Gwamna Muhammad Bello Matawalle na jihar Zamfara ya umarci baki ɗaya masarautun jihar da su nemi sahalewar gwamnati kafin naɗa wa wani rawanin Sarauta.

Gwamnan ya bayyana haka ne a wata sanarwa da babban mai taimaka masa ta ɓangaren yaɗa labarai, Zailani Bappa, ya fitar, kamar yadda rahoton Daily Trust ya tabbatar.

Gwamna Bello Matawalle na Zamfara.
Da Ɗumi-Ɗumi: Gwamna Matawalle ya haramta wa sarakunan Zamfara naɗin Sarauta Hoto: Bello Matawalle/facebook
Asali: Facebook

A rahoton Channels tv, gwamna Bello Matawalle ya ce:

Kara karanta wannan

2023: Hukuncin tsawon rayuwa da INEC take son a yi wa yan siyasa masu siyan kuri'u a Najeriya

"Baki ɗaya Sarakuna, manyan hakimai da hakimai da ke faɗin jiha, muna umartan su da su nemi izinin gwamnatin jihar kafin naɗa wa kowane mutum rawanin sarauta."

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

"Wannan matakin ya zama wajibi domin sa ido kan naɗin sarautar da ake yi ba tare da la'akari ba da kuma yuwuwar zubar da ƙimar masarautu."
"Saboda haka daga yanzu, babu wani Sarki, babban Hakimi ko Ƙarami da zai naɗa ko waye wani muƙamin sarauta ba tare da samun sahalewa da amincewa a hukumance daga gwamnatin jiha ba."

Wane hukunci gwamnati ta tanda ga masu kunnen ƙashi?

Bugu da ƙari, gwamnan ya ƙara da gargaɗin baki ɗaya sarakunan jihar cewa bin wannan umarni ya zama tilas kuma duk wanda ya yi kunnen gashi zai ga abinda zai biyo baya.

"Biyayya ga wannan umarnin ya zama tilas kuma duk wanda ya tsallake shi gwamnati zata tsawatar masa tsawa ta gaske."

Kara karanta wannan

'Yan bindiga sun kutsa har cikin gida, sun sace wani babban Basarake a arewa

Legit.ng Hausa ta rahoto muku yadda masarautar Yandoto ta naɗa ƙasurgumin ɗan ta'adɗa, Adamu Aleru, wata sarauta, lamarin da ya ta da ƙura a ciki da wajen jihar Zamfara.

A wani labarin kuma kun ji cewa Kotun ɗaukaka ƙara ta yanke hukunci kan sauya sheƙar gwamna Matawalle

Kotun ɗaukaka ƙara da ke zaman ta a birnin Shehu ta ce babu ta yadda gwamna zai rasa kujerarsa saboda ya sauya sheka zuwa wata jam'iyya.

Da take yanke hukunci, ta tabbatar da hukuncin farko da babbar Kotun tarayya ta Gusau ta yanke kan gwamna Bello Matawalle.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262