Yanzu-yanzu: Lauyan Nnamdi Kanu ya musanta jita-jitar da ake yadawa cewa shugaban kungiyar IPOB ya bata
- Babban Lauyan Nnamdi Kanu Ifeanyi Ejiofor ya karyata jita-jitan da ake yadawa na cewa shugaban IPOB ya ba ce
- A ranar Alhamis tawagar lauyoyin dake kare shugaban kungiyar IPOB suka kai mishi ziyara a hedkwatar DSS
- Lauyoyi Nnamdi Kanu sun yi kira ga mabiyan sa da su yi watsi da karerayin da makiya ke yadawa akan shugaban su
ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit
Abuja - Ifeanyi Ejiofor, Babban Lauyan Nnamdi Kanu da masu fafutukar kafa kasar Biafra (IPOB) a ranar Juma’a ya ce sabanin jita-jitar da ake yadawa, wanda yake karewa bai yi batan dabo ba a hannun hukumar tsaro ta farin kaya (DSS). Rahoton INDPENDENT
Ejiofor ya bayyana hakan ne a cikin wata sanarwa da wani kafar yada labarai ta yanar gizo.
Ya bayyana cewa tawagar lauyoyin Kanu sun ziyarce shi a ranar Alhamis a hedkwatar hukumar DSS da ke Abuja.
MUHIMMAN BAYANI
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
“Don Allah UMUCHINEKE, ku yi watsi da sakon faifan sauti da makiyan mutanenmu ke yadawa na cewa ONYENDU MAZI NNAMDI KANU ya bata a ofishin DSS.
“Bayanan karya ne, kuma ya kamata a yi watsi da ita gaba daya daga UMUCHINEKE.
“A gaskiya, a jiya ne kotu ta bayar da umarnin gudanar da ziyarar ta yau da kullum, kuma ONENDU ya shafe lokaci tare da wadanda suka ziyarce shi.
Idan aka kara kai wani hari, Za Mu Sayi Bindiga mu ba Mutanen mu – Akeredolu
A wani labar kuma, Gwamnan jihar Ondo Rotimi Akeredolu ya bayyana cewa zai baiwa al’ummar jihar Ondo makamai domin kare kansu idan ‘yan ta’adda suka sake kai hari a jihar.
Ya bayyana hakan ne a ranar Juma’ar da ta gabata yayin da yake gabatar da motoci 50 da suka dace da jami’an tsaro a jihar, ciki har da kungiyar tsaro ta jihar Ondo, wacce aka fi sani da Amotekun.
Asali: Legit.ng