Fursunonin da aka yanke musu hukuncin kisa a Ribas sun kai 442
- Fursunoni 442 wanda ya hada da mata suke jira a yanke musu hukuncin kisa a gidajen yari jihar Ribas
- Gidajen yarin jihar Ribas na dauke da akalla fursunoni 4,403 inji Kwanturolan gidajen yari na jihar
- Kwanturolan gidajen yarin jihar Ribas ya dau alwashin hada kai da yansanda da hukumar shariar wajen rage cunkoson gidajen yarin jihar
Jihar Ribas - Hukumar gidan Yarin Najeriya reshen jihar Ribas ta zata hada gwiwa da hukumomin gwamanti domin rage cunkoson gidajen yarin jihar, inda ya ce gidajen yarin na dauke da fursunoni 4,403. Rahoton jaridar PUNCH
Daga cikin gidajen yarin jihar Ribas guda hudu da ke birnin Fatakwal, na Degema, Ahoada da Elele, suna da fursunoni guda 442 na jiran a zartar musu da hukuncin kisa, daga cikin su har da mata.
Kwanturolan gidajen yari na jihar Ribas, Felix Lawrence ne ya bayyana hakan a lokacin da yake zantawa da manema labarai a Fatakwal jim kadan bayan kammala bikin shigiwar sabon Kontrola da Ficewar tsohon kwanturola daga jihar.
Lawrence yace hukumar su za ta hada gwiwa da bangaren shari’a na jihar Ribas da ‘yan sanda wajen daukan matakin rage cunkoso a gidajen Yarin jihar.
DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka
Harin gidan yarin Kuje: Buhari da shuwagabannin tsaro sun gaza, Ndume
A wani labari, Abuja - Shugaban kwamitin majalisar dattawa akan harkokin soji, Ali Ndume, ya caccaki shugaban kasa Muhammadu Buhari da hafsoshin tsaron kasar kan tabarbarewar tsaro a kasar. Rahoton Premium Times
Mista Ndume, dan majalisar dattawa na jam’iyyar APC mai wakiltar Borno ta Kudu, dangane da mummunan harin da aka kai gidan yarin Kuje a ranar Talata, ya ce shugabancin kasar ya gaza a babban kudirin sa na ga ‘yan kasa.
Asali: Legit.ng