An damke mai gadi kan laifin dirkawa diyar maigidansa cikin a Legas

An damke mai gadi kan laifin dirkawa diyar maigidansa cikin a Legas

  • Maigadi ya shiga hannu bayan damkeshi yana take diyar maigidansa har ya dirka mata ciki
  • Kakakin hukumar yan sandan jihar Legas yace yarinyar yar shekara 15 ce kuma laifi ne ya aikata ko da ko da amincewarta
  • Wata kungiyar kare hakkin hara da marasa galihu ne suka shigar da kararsa wajen hukumar

Legas - Hukumar yan sandan Najeriya, shiyyar Ikorodu a jihar Legas ta damke wani mai tsaron gida, Samuel Maikasuwa, kan laifin dirkawa diyar maigidansa ciki.

Wata Kungiyar kare hakkin yara tace Ana zargin Samuel da kwanciya da yarinyar yar shekara 15, rahoton Sahara Reporters.

Matashin ya kasance mai gadin gidan uban yarinyar mai suna Fadiji.

Kungiyar ta ACVPN ta bayyana cewa an taba damke matashin yana lalata da yarinyar bara amma a gargadesa kada ya kara.

Kara karanta wannan

2023: Gwamnonin APC sun zauna, sun yi shawarwari kan yankin da zai kawo abokin tafiyar Tinubu

Tace:

“Matashin da ya yiwa yarinya yar shekara 15 fyade sunansa Samuel Maikasuwa dan shekara 20. Dan garin Abaji daga Abuja.”

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

“Ya kasance mai gadi a gidan Mr Fadiji. An taba kamashi da ita bara kuma aka gargadeshi kada ya sake kusantar yarinyar kuma ya bada hakuri.”
“An garkameshi a ofishin yan sandan Ikorodu, Igbogbo.”
Maikasuwa
An damke mai gadi kan laifin dirkawa diyar maigidansa cikin a Legas Hoto: Sahara Reporters
Asali: Facebook

Kakakin hukumar yan sandan jihar, Benjamin Hundryin, ya tabbatar da damkeshi.

Yace:

“Ko shakka babu. Amma ba wai kawai yayi matanciki bane. A doka fyade ne.Saboda yar yarinya ce. Har yanzu ana bincike.”

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel