Jam’ian DSS sun ceto Almajirai 21 da aka turke a Cocin ECWA ana kokarin mayar da su Kirista a Jos
- Jam’ian hukumar DSS ta bankado wani gidan coci da ake tilasta yara shiga addinin Kirista a Jos
- Hukumar ta ceto yara 21 da aka gano cikin gidan mallakin cocin ECWA bayan watanni suna turke
- Daya daga cikin yaran ne ya samu daman tserewa daga gidan ya kai kara masallacin garin Jos
Jos - Jam’ian hukumar DSS sun kai simame wani gida dake JMDB quarters, unguwar Tudun Wada dake karamar hukumar Jos ta Arewa inda ta ceto yara 21, cikinsu har da Almajirai.
Kungiyar Jama’atu Nasril Islam JNI ya laburtawa manema labarai cewa yaran sun yi bayanin yadda aka garkamesu cikin gidan ana kokarin tilastasu komawa addinin Kirista, rahoton Daily Trust.
Sakatare Janar na cocin ECWA, Rabaran Yunusa Nmadum ya tabbatar lallai gidan da DSS ta kai simame mallakin cocinsa ne amma ya musanta cewa ana amfani da gidan wajen tilasta mutane shiga addinin Kirista.
'Yan bindiga sun sake kai sabon kazamin hari Kaduna, sun kashe jami'an tsaro sun sace dandazon mutane
Rahoton ya kara cewa an tara yaran a gidan ne bayan kwasosu daga jihohi daban-daban zuwa Jos.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Diraktan hukumar agajin Jama’atu, Danjuma Khalid, ya bayyana cewa an bankado gidan ne lokacin da daya daga cikin yaran mai suna AbdulRahman Hussaini, ya tsere.
Yace an ajiye yaran tsawon watanni 8 a gidan.
Yace:
“A ranar 13 ga Yuni, wasu yara ciki har da AbdulRahman da suka samu guduwa daga gidan suka taru a Babban Masallaci sun kawo karar wani gida da ake tilasta yara zama Kirista a wani cocin ECWA dake Jos.”
“ Ranar 14 ga Yuni muka kai kara wajen DSS, jihar Plateau, kuma yaron sukayi bayanin yadda aka kwasosu daga Gombe zuwa Jos da yadda ya gudu daga gidan dake Tudun Wada.”
“Kai tsaye DSS ta dau mataki. Jam’ianta suka tafi gidan tare da yaron kuma suka ceto yara 21.”
Asali: Legit.ng